Abubuwa 12 dake sa mace ta zama Tauraruwar girki

           Abubuwa 12 dake sa mace ta zama Tauraruwar girki


      

Mace Mai koyon girki Mai dadi, mata Mai kunya


     Assalamu alaikum warahamatullah wabarakatuhu kamr yadda taken post din nan ya gabata zamuyi Magana ne inshallahu akan abubuwa guda 12  wadanda ke sa mace ta zama tauraruwa wajen yin girki, tabbas mace sai da hirki domin idan uwar gida bata iya girki mai dadi ba akwai matsala a wajen mai gida, don ma kusan yan uwa mata ya kamata su fahimta cewa iya girki yana kara dankon soayayya a wurin mai gida bayan Kwalliya ko kafinta ma/

    Domin mace sai da iya girki in bata iya giki ba a gidan miji to ay kusan kamar ta rako mata kawai ne

     kuma ma wannan matsala ita ta ke sa mai gida ma idan yaga wadda ta burge shi ya aure ta kekuma  daga nan an kwace maki masoyi. To yanzu zamu lisssafa abubuwan kamar haka.


Abubuwa 12 dake sa mace ta zama Tauraruwar girki


1.      Idan kina cikin dafa miyar tumatur sai aka samu matsala ta kone, to zaki sauke ne sai ki sauya tukunyar  sannan kuma ki kara sugar kadan kadan har said an danon kaurin ya tafi.

2.      Idan kika samu kuskure gishiri yay yawa a cikin abinci ko a cikin miyarki, abinda zakiyi anan shine ki fera dankali kijefa a cikin dankalin inshallahu zai shanye gishirin.

3.      A lokacin da abincinci yak one yake kauri to kisamu biredi mai yanka yanka guda daya sai ki dora a kan abincin, biredin zai nade kaurin, ammafa a nan sai kinyi hankali karki kankaro wajen da ya kone yayin da kike diban abincin.

4.      Idan kuma aka samu matsala mai ne yayi yawa a cikin miya to zaki jefa kankara yar karama zakiga ta maido man wuri daya sai kawai ki kwashe.
5.      Idan kuma baki so dankalin da kika ajiye a kan buhu ya fara tsuro to kisamu tufa guda daya ki saka a cikin buhun.
6.      Idan kishirinki yafara curewa saboda damshi,to ki jefa kwarorin shinkafa a ciki, su zasu shanye damshin da ikon Allah.
7.      Kada ki ajiye ayaba yuri daya da sauran kayan itace domin ita tana da wani iska data ke saki wanda ke sa su nuna da wuri wanda hakan na iya sa su lalace da wuri.
8.      Idan kika hada kofuka guda biyu na gilashi wanda kika gaza rabasu to domin ki samu saukin rabasu ki saka kankara a na saman shima na kasan ki saka shi a cikin rowan dumi, abun da ke faruwa shine na kasan zai fidda na saman ya tsuke wanda zai saukaka wajen raba su.
9.      Kada ki rinka ajiye tumatur da lemun tsami a fridge domin sanyi yana rage ma tumatur da lemu kamshi da dandano.
10.   Idan cinnaku  sun addabe ke to yadda za ki yi shine ki nemi hudar da suke fitowa ki shfa basilin a wurin baza su iya tsallakawa ba. Idan kuma ta karkashin kofa suke shigowa, toki samo allin ki sai ki ja layi shima baza su iya tsallakawa ba.
11.   Idan kuma kina son amfani da mai wanda kikai amfani da shi a wata suya a baya sai yanzu ma kikaga kina son kara amfani da shi amma ba ki son kamshin abunda kika soya a baya to yadda zakiyi shine ki soya danyar citta kadan a ciki inshallahu zai kawar da kamshi.

12.   Idan kina amfni ne da tukunyar aluminium kuma ta fara kodewa, dudda dai na san kinsan yadda zaki iya wanke bayan tukunyar yayi sheik to amma cikin fah? To a nan abunda zakiyi shina ki zuba bawon tufa a ciki da ruwa kid an dafa zai rage kodewa inshallahu.

    Wasu daga cikin post din hausawasite yaddaakan  ake Girki Mai dadi 

Ga wadansu daga cikin list din da aka koya abinci kala kala a wannan website din fon karantawa.

 Yadda ake gika abinci  a lissafe

bayan haka kuma akwai post na koyon sana’a wanda muke yi a wannan website din misali ana iya duba yadda ake hada man shafawa ga kuma bayani akan yadda za’a sayi sinadaran.

A karshe

Alhamdullilah, to jama’a a nan ne muka zo karshen wannan post din wadda muka sama taken abubuwa guda sha biyu (12) wadan da ke sa mace ta zama tauraruwa a wajen girki muna fatan zaa cigaba da kasancewa a tare da mu a wannan website mai albarka kuma duk wadda keda tambaya ko Karin bayani to tana iya yi a comment section, mungode.