Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu jama’a kamar yadda aka sani a wannan website mai albarka wadda keda taken address www.hausawasite.com.ng muna koya yadda ake abubuwan da mu gurinmu shine a iya don samun sana’a koma don amfanin gida. To a yau ma inshaallah mun taho da wata tsaraba mai girma wadda itace yadda ake hada abun kyautata kamshin iska a hausance ko mu ce air freshner a takaice to kamar yadda muka saba har kullum muna fara lissafa kayan hadin wato kayan da zaa sawo a kasuwa sannan mu je ga yadda ake hada abubuwan kabkidaya.
Shima wannan abun kyautata kamshin iska(air freshner) ana bukatar sinadarai kamar haka, amma fa a kula nan a awon mu ne ya danganta ga yadda mutum yake son yayi.
In baka karanta yadda ake hada man shafawa ba na saidawa shima akwai shi inda muka koya yadda ake fara kasuwancin hada man shafawar sai ka duba to bari muga lissafin sinadaran da mutum ke bukata in yana son ya hada air freshner.
Sinadaran hada air freshner a lissafe
1. Turare => ana bukatar kwalba hudu (4) mai kamshin dadi ko wane irine.
2. Isanol => shikuma ana bukatar awo biyar (5).
3. Mensol => shima ana bukatar kulli daya (1) shine karfin kamshi.
4. Antisol => shi ana bukatar awo daya (1).
5. Farin sikina => ana bukatar awo (3) ne.
To baccin an samo ko an sawo sinadan da muka zayyan a sama to bari muje ga yadda ake hadda wato aynafin su sinadaran.
Yadda ake Hadawa
Da farko dai zaa narka Antisol da ruwa, sannan sai a zuba mensol a cikin turare ya narke, daga nan zaa zuba isanol a cikin wurin da zaa yi hadin kayan, sannan kuma sai a zuba wato shi mensol din da aka narke a cikin turaren sai a motsa su sosai har sai sun motsu sosai har kamar tsawon akalla minti goma (10), sannan sai a zuba shi a hankali a narkaken antisol din, kana motsawa, sa farin sikina, sa farin sikina da yan ruwa, sa su a cikin wurin hadin motsa su, sai a kara ruwa , ana sawa ana motsawa, tsawon minti goma, daga nan kuma sai a zuba a cikin abinda zaa kai kasuwa wato kwallabe shkenan.
To Alhamdulillah an kam abun kyautata kamshin iska, wanda ked a tambaya ko Karin bayani yana iya yi a comment section wanda ke akasa, kuma muna fatan zaa cigaba da kasancewa a tare da mu a www.hausawasite.com.ng mungode.
ADDRESHIN DA ZA’A SAMU SINARAN
Lambar waya
+2349037157675+2349072783217Websitekubiyomu a facebook
Email address
Tura a shafukar sada Zumunta
↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓
Author Profile

Latest entries
GirkiNovember 25, 2023YADDA AKE MOIMOI (ALALA) DA MIYAR KODA
UncategorizedNovember 24, 2023Yadda ake sarrafa kifi
UncategorizedNovember 15, 2023Ciwon Snyi: Muhimman Abubuwan da ya Kamata ka sani akan Sanyi
UncategorizedNovember 12, 2023Yadda ake miyar yalo