Skip to content
Home » Yadda ake hada ingantaccen sabilin ruwa

Yadda ake hada ingantaccen sabilin ruwa

       Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu muna maku barka da zuwa wannan site mai albarka mai suna Hausawa Site, kamar yadda aka saba  kamar kullun muna kawo maku post masu amfani kamar na ilimantarwa na sana’oi da ma sauransu  to a yau ma inshallahu mun zo ma ku da zarabar yadda hada sabilin ruwa (200 lita )  mai inganci, to kamar yadda kowa ya riga ya san anfanin sabi ba ma wai kawai na ruwa ba ana amfani ne da shi domin tsaftace abubuwan amfani ko kuma wuri.

      To domin hada wannan sabilin rowan a cikin wannan post din zamu lissafa kayan da za a nemo a kasuwa, yadda zaa tsima sinadaran da  kuma yadda ake hada su, to amma da farko zamu yi bayani ne akan sinadaran da zaa nemo ko ince kayan da zaa sawo.

Sinadaran da ake Bukata

A kula a nan in muka ce awo ya danganta ne akan koma wane abu ne kake/kike amfani da shi.

1.      Antisol => anan bukatar Awo biyu (2).
2.      Salonic Acid => Awo biyar (5).
3.      Kastic soda => Awo shidda (6).
4.      Soda Ash => Awo biyu (2).
5.      S.t.t.p => Awo biyu (2).
6.      Tazafon ko SLS => Awo biyu (2).
7.      Fomalin => Awo  daya bisa takwas (1/8).
8.      Kala => yadda ake so.
9.      Turarae => rabin kwalba.
10.   Ruwa => kashi dari (100%).

To kamar yadda muka lissafa sinadaran yanzu kuma zamu ze akan matakan da ake bi wajen  tsima sinadaran kafin mu je ga yadda ake hadawa.

Matakan Tsima Sinadarai

       Da farko za’a dauko antisol ne a narka shi da kashi dari (100%) na ruwa har tsawona wa ashirin da hudu (24) , amma fa idan za’ayi amfani ne da wani inji ko machine za’a burka shi to ba sai ya kai tsawon wannan lokacin ba.
·      A bi matakin tsimin kastic soda din sabilinwanki (danna ka ga na sabilin wanki mun yi shi a baya) a tuna cewaar karatun hairomitar fa ba iri daya bane ba.

Bayan an kammala matakin tsimin yanzu kuma zamu je ga matakin yadda ake hadawa.

Yadda Ake Hadawa

Dafarko dai za’a kwada awo shidda (6) na kastic soda , sa soda ash awo biyu (2) da awo biyar(5) na salfonik acid a motse su.
Sa tazafon ko SLS awo biyu (2) a motse ita motse su sosai har tsawon mini biyar (5).
Sa s.t.t.p a motse,

Sa formalin awo 1/8 a motse sannan a hada su cikin tsimammen antisol a motse su sosai.
Da ga nan kuma sai a sa turare da kala yadda ake so a motse sosai har sawon minti biyar sannan sai a bar shi yayi sanyi daga nan kuma sai a gyara domin saidawa ko amfanin gida, amma bari muji kai/ke ya naka yake?.

      Alhamdulillahi sabilin ruwa ya kammalu muna fatan kunji dadin wannan post din kuma kuma duk mai tambaya yayi ta a comment section wabada yake a kasa. Muna fatan zaa cigaba da kasancewa da Hausawa site mungode.