Skip to content
Home » yadda ake hada ingantaccen shampo na gashi

yadda ake hada ingantaccen shampo na gashi

yadda ake hada ingantaccen   shampo na gashi


                   


.  Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu barkanku da zuwa a wannan shafi mai albarka, a yau inshallahu zamuyi Magana ne akan yaadda ake hade shampoo na gashi kamar yadda taken post din ya gabata.

               kamar  yadda kuka sani a wannan website ko ince blog kulun muna kokari ne akan yadda zamu rika koyar da mutane abubuwa dakuma fadakar dasu akan abubuwan da ke faruwa a duniya, to shidai kamar yadda aka sani ana amfani ne da shampoo domin kyaran ko ince tsaftace gashi ne.

               kuma inshallah indai aka bimu ahankali a cikin wannan post zaa a iya hada shampon da ba wai kawai ayi amfani das hi ba a gida a’a har ma a sayda domin yan daka cikin burin wannan site din ta taimaka wajen samar da aikin yi ga matasa.  To zamu lissafa kayan da zaa nema a kasuwa da Kuma yadda zaa a hada kayan ko ince sinadaran amma yanxu zamu fara lissafa .


       
            Yadda ake hada fried rice


Sinadaran Da Ake Bukata


1.      Salfonic acid: kashi ashirin da biyar (25%)
2.      Sodium laril salfet: ana bukatar kashi biyar (5%) bisa dari
3.      Soda ash :ana bukatar kashi biyar (5%) bisa dari.
4.      Firofelingilecol : shima kashi biyar (5%)  bisa dari.
5.      Natiroso: ana bukatar kashi biyar (5%) bisa dari.
6.      Misel Farabin ko Formalin : kashi daya (1%) bisa dari.
7.      Kala: yadda ake so .
8.      Turare : shima a sa yadda ake so.
9.      Ruwa : kashi talatin da shidda(36%)bisa dari.

Matakan tsima sinadarai

Mataki na farko

Auna keji ukku (3) na ruwa tare sda keji daya (1) na soda ash, gauraya su, a aje suyi awa (24).

Mataki na biyu

Bayan kamar tsawon awa 24  dauki hadiromita a ciki don samun  daidai lamba 1225.


Yadda ake hadawa shampoo din


Dafarko dai zaa a auna kashi 5% bisa dari na soda ash, a hada shi da salfonic acid kashi 25% bisa dari ,sai a motsa  su sosai,
Sai a hada kashi 5% bisa dari na SLS wato sodium lari salfet, daganan kuma sai a hada farofelin gelukol kashi 5% bisa dari a motsa.

Hada nitroso kashi 5% bisa dari a motsa .

Hada  da ruwa lita 36 motsa sosai, sannan hada turare da kala yadda ake so, a tsara su don saidawa ko amfani a gida .

Shikenan Alhamdulillah muna fatan kunji dadin post din nan kuma ku cigaba da kasancewa tare da mu a wannan website mai albarka mai adreshin www.hausawasite.com.ng kuma ina jiran commen din kowa kai/ke mai karatu ya ka hada rubuta comment a comment section.