Skip to content
Home » Yadda ake hada sabulun wanka a saukake

Yadda ake hada sabulun wanka a saukake

 

Yadda Ake hada sabulun wanka.

Yadda Ake hada sabulun wanka wannan post din yake maga akai a shirts shi ne don duk wanda ya karanta 
Ya kasance Shima yana iya hada sabulun wanka inshallah in dai tabi steps din.

      Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu kamar yadda  taken post na wannan shafin ya gabata a yauma inshallahu zamuyi Magana ne akan yadda ake hada sabilin wanka mai inganci, ta hanya mai sauki wadda kowa zai iya fahimta.


To kamar yadda kuka sani shidai sabilin wanka yana daya daga cikin abubuwa wadanda ake yawan amfani da su a kullun domin kowa yana son yayi  tsafta.

kusanma tsafta wajibi ne domin in ba tsafta  ko ma kusan ince duka ayyukanaddini basu inganta, shi yasa idan kuka lura ana amfani da sabilin wankadon a tsaftace jiki, yawn anfani dashi sabilin wanka shi ya sa yawancin masu sana’ar hada sabili suke samun kudi sosai, a cikin wannan post din zamu yi bayani sosai ta hanyar da koma wanda ke da sha’awar yin na sayarwa zai iya yi domin ya samu sana’a mai karfi, bari mu je zuwa sinadaran da ake so, tsimin sinadaran da kuma yadda ake hada sinadaran.

                                     siandaran da ake bukata waje hadawa

wadannan chemicals din da zan lissafa yanzu sune mutum ya sawo su a kasuwa gasu kamar haka:

                  1.      P.k oil: ko kuma a hausance man cinda zugu, ana bukatar Awo shidda (6).


2.      Castic soda: ita wannan wato castic soda (shine tushen sabili) ana bukatar ta Awo ukku(3).

3.      Soda ash: shi wannan sinadarin wato soda ash yana sa kumfa kuma ana bukatar Awo daya(1) ne.

4.      S.T.P.P:  anan ana bukatar Awo Daya bisa tawas(1/8) ne (yana taimakwa wajen kumfa).

5.   Borasshima kusa ana bukatar  Awo Daya bisa takwas(1/8)shima (yana taimakwa wajen kumfa).

6.      Colour (kala): kala ita za’a zuba ta ne yadda ale son abun ya kasance ne amma fa kar wadda take narkewa a cikin mai.

7.      Silket : shi za’a sa Awo biyu bisa takwas(2/8) ne shi yana hade sinadarai ne.

8.      Turare : shima kusan kamar kala ne ana sa shi yadda ake son sabilin ya kasance.

9.  Maganin kashe kwayoyin cuta : shima yadda kakeso haka za’a zuba.


                                                                Tsimin Sinadarai  
        
Mataki na Daya:
Da farko za’a awna keji ukku (3) na ruwa sannan sai a gauraya shi da keji daya(1) na kastic soda har  tsawon awa ashirin da hudu(24).

                               Mataki na Biyu:

                            A wannan mataki shima kusan kamar na daya ne zaa yi irin awon da akai a sama wato zaa yima soda ash itama har tsawon awa ashirin da hudu(24).

                            Mataki na Ukku:

Bayan awa ashirin da hudu(24), dauki awon hadirometer a cikin ya bada daidai dad a 1275, idan ya wuce 1275 yana nuna cewar ruwa yayi yawa sai a kara dan garin kastic soda don lambar tai daidai ta, idan kuwa ya kasa to yana nuna cewar abin sinadarin yayi karfi da yawa sai a kara dan ruwa ta yanda zaa samu daidai da 1275.

                         Mataki na Hudu:

Yi amfani da yadda kai a sama ma S.T.P.P


Yadda ake hadawa

1.   Zuba aunannen man awo 6 a cikin abinda za’ayi hadin sabilin a ciki asa kala a motse sosai sannan a tace. kulura idan man mai daskarewa ne to, a dan tada shi da wuta; 


2.     Sa kastic soda awo ukku [3] a motse

3.      Sa soda Ash awo daya [1] amman idan ana cikin motsawa zaa rika zubawa.

5.      Sa S.T.T.P Awo 1/8  a motsa.

6.     Sa Siliket Awo 2/8 a motsa

7.   sa maganin kashe kwayoyin cuta yadda akeso, asa turare a motsa su ga baki daya sosai;

8.  Juye cikin abin juyewar, barshi yadan sha iska sai a yanyanka a buga hatimi [stamp] sannan sai anade asa acikin kwali a saida.

      Alhamdulillah Sabuli ya kamala, domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan zaa cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.