Skip to content
Home » yadda ake hada sabulun wanki

yadda ake hada sabulun wanki

Yadda ake hada sabulun wanki.

 Yadda Ake hada sabulun wanki a cikin steps masu sauki, shi wannan sabulun wanki da zaay magana kanshi kowa yana iya kokari ya hada shi lafiya lau inshallah in aka bi steps din, wannan wanda zamuyi magana a cikin post din nan standard sabulu ne ga masu son koyon sabulu na yan kasuwa wadanda so suke su saida su karanta post din yadda ake sabulun wanki na saidawa,

   Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu kamar yadda  taken post na wannan shafin ya gabata a yau inshallahu zamuyi Magana ne akan yadda ake hada sabilin wanki mai inganci, ta hanya mai sauki wadda kowa zai iya fahimta.

       To kamar yadda kuka sani shidai sabilin wanki yana daya daga cikin abubuwa wadanda ake yawan amfani da su a kullun domin kowa yana son yayi  tsafta kuma kusanma wajibi ne domin in ba tsafta kusan ma yawanci ko ma kusan ince duke ayyukan addini basu inganta, shi yasa idan kuka lura ana amfani da sabilin wanki don tsaftace kaya , yawan anfani dashi sabilin wanki shi ya sa yawancin masu sana’ar hada sabili suke samun kudi sosai, a cikin wannan post din zamu yi bayani sosai ta hanyar da koma wanda ke da sha’awar yin na sayarwa zai iya yi domin ya samu sana’a mai karfi, kar mu cika surutu hakanan bari mu je zuwa sinadaran da ake so, tsimin sinadaran da kuma yadda ake hada sinadaran.

Yadda ake sabulu                     Sinadaran da ake buakata don hada sabulin wanki


Wadannan sinadaran ko ince chemicals d azan lissafa a kasa sune ake so a sawo a kasuwa zamu lissafa su, ga su kamar haka:-

1.      P.k oil: ko kuma a hausance maganin cinda zugu, ana bukatar Awo shidda (6).

2.      Castic soda: ita wannan wato castic soda (shine tushen sabili) ana bukatar ta Awo ukku(3).

3.      Soda ash: shi wannan sinadarin wato soda ash yana sa kumfa kuma ana bukatar Awo daya(1) ne.

4.      S.T.P.P:  anan ana bukatar Awo Daya bisa tawas(1/8) ne (yana taimakwa wajen kumfa).

5.      Salfet (sulphate): shima kusa ana bukatar  Awo Daya bisa takwas(1/8) shima (yana taimakwa wajen kumfa).

6.      Colour (kala): kala ita za’a zuba ta ne yadda ale son abun ya kasance ne amma fa kar wadda take narkewa a cikin mai.

7.      Silket : shi za’a sa Awo biyu bisa takwas(2/8) ne shi yana hade sinadarai ne.

8.      Turare : shima kusan kamar kala ne ana sa shi yadda ake son sabilin ya kasance.

karanta:                 Yadda ake cake cikin steps masu sauki

                             Yadda uwar gida zatai fried rice
                            Abubuwa 12 dake mace tazama tauraruwar girki
                             yadda ake hada tsire
            yadda ake samosa

             Download Ruwanbagaja pdf
             yadda ake hada yam-ball
             yadda ake connecting din xender da android.
             yadda ake hada yamball
             yadda ake fried rice 
             yadda ake spring rolls da meat pie   
             yadda ake yin pizza        

           yadda ake hada samosa

              Tsimin Sinadaran da ake hada sabulun wanki da su     

   Mataki na Daya:

Da farko za’a awna keji ukku (3) na ruwa sannan sai a gauraya shi da keji daya(1) na kastic soda har  tsawon awa ashirin da hudu(24).

                               Mataki na Biyu:

                            A wannan mataki shima kusan kamar na daya ne zaa yi irin awon da akai a sama wato zaa yima soda ash itama har tsawon awa ashirin da hudu(24).

                            Mataki na Ukku:


Bayan awa ashirin da hudu(24), dauki awon hadirometer a cikin ya bada daidai dad a 1275, idan ya wuce 1275 yana nuna cewar ruwa yayi yawa sai a kara dan garin kastic soda don lambar tai daidai ta, idan kuwa ya kasa to yana nuna cewar abin sinadarin yayi karfi da yawa sai a kara dan ruwa ta yanda zaa samu daidai da 1275.

                         Mataki na Hudu:


Yi amfani da yadda kai a sama ma S.T.P.P.

kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai  Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu

Yadda ake hadawa

1.      Auna awo shida na man P.K.O ko M.Y,C sannan sai a sa kala yadda ake so a ciki, sai a motsa har sai ya motsu sosai sannan sai a tace.

2.      Idan man mai daskarewa ne (kamar konturola, P.K.O da sauransu ), dan narkeshi akan wuta kadan sai a juye shi a cikin abinda zaay hadin a ciki.

3.      Sa kastic soda awo ukku(3) a motse da soda ash awo daya(1) a ciki sannan a motes soda ash awo daya a ciki.

4.      Sa S.T.P.P awo daya bisa takwas 1/8 a motse, sannan a sa salfet awo 1/8 da silket awo 2/8 a motsa.

5.      Sa turare rurare yanda akeso sannan a motsa su sosai.

6.      Juya a cikin abinda ka tanada ya dan bushe sai kuma a yayyanka a kuma buga hatimi sannan a sirya su domin saydawa.

Alhamdulillah Sabuli ya kamala, domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan zaa cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.