Skip to content
Home » Yadda ake maida page din website ya zama pdf a computer ko a waya.

Yadda ake maida page din website ya zama pdf a computer ko a waya.


         Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu to jama’a kamar yadda aka saba a wannan website ta Hausawa Site muna yin post ne wanda yake koyar da mutane game da kimiyya da fasaha, girki, sanwa da ma sauran al’amurra na rayuwa to a yau ma inshallahu mun zo maku da wani sabon post ne akan yadda zaka maida shafin website a matsayin pdf domin ka rika karantawa.


  Akwai post din da nay akan yadda ake bude website kana iya duba shi,To adai shi wannan post din yana maganar hada pdf ne daga page din website kuma  zamu raba abun ne kamar maki biyu ne, yadda zakai a computer da yadda zakai a wayar ka, to amma bari mu fara  a kan yadda zakai a computer.


karanta:            Yadda ake cake cikin steps masu sauki
                             Yadda uwar gida zatai fried rice
                            Abubuwa 12 dake mace tazama tauraruwar girki

                             yadda ake hada tsire

            yadda ake samosa

             Download Ruwanbagaja pdf
             yadda ake hada yam-ball
             yadda ake connecting din xender da android.
             yadda ake hada yamball
             yadda ake fried rice 
             yadda ake spring rolls da meat pie   
             yadda ake yin pizza        
           yadda ake hada samosa

           Download littafin Ruwanbagaja pdf  
  
           Yadda ake bude website

                                              Matakan Computer


1. Da farko za ka ziyarci shafin website wanda kake so ka maida shi littafin pdf din.

2. Sai ka danna “CNT+P (wato control p)” to idan ka danna a default yadda sukai print ne to sai ka maida destination shi save as pdf.

3.  Sai ka danna “save” za kaga ya nuna ma ka zabi folder wadda zakai saving din shi sai ka danna “ok” shikenan.

    To  daka yi save din shikenan kana iya bude shi a duk lokacin da kake son ka bude shi as pdf dinka.
   
    To bari muje ga yadda ake yi a waya, to a waya ana yi fa ne kawaia ta hanyar amfani da chrome browser idan kana da chrome a wayar ka kana iya bin wadannan matakan wanda zamu lissafa a kasa.
                                            Matakan Waya
1. Da farko dai zaka shiga chrome sai ka bude page din website dinda kake son maida shi pdf.

2. Sai ka danna share.

3. Sai ka danna option na hannun dama (wadannan abubuwan kwara ukku na sama daga gefen dama).

4. Sai ka zabi share a optrions din kanna.

5. zaakaga ya nuna ma icons hadda na print sai ka danna print din.

6. Daga nan zai nuna ma preview sai ka danna pdf daga sama a hannun dama.

7. Sai ka danna “Save”.

        Ka gama, daga nan kana iya bude pdf din ka koda yaushe kake so, muna fatan za’a cigaba da kasancewa tare da mu a wannan website mai suna Hausawa Site ko don samun bayanai na ilimantarwa fadakarwa dama sauransu, kana iya search din mu a google daka sa sunan ishaallahu zaka samemu, kana iya subscribe da email dinka don samun sabbin post idan mukayi.

       Wanda bai gane wani abu ba yayi comment, mungode.
Alhamdulillah.