zamu kawo muku bayanin yadda ake yin bura bisko tare dani Ismail wanda zai jagoraci shirin Inshaallah ku biyo mu domin ganin yadda ake yi
Abubuwanda ake bukatar uwar gida ta sawo
* Gero ko Masara
* Man gyada
* Gishiri
* Ruwa
Yadda ake hadawa
Idan kika gyara geronki ko masararki soasai zaki kai a niko maki ita in an niko miki ita sai ki tankade ki fidda garin, sai ki dauko madambacinki bisa wuta ki yayyafa ruwa ciki, sai ki bashi lokaci da kika san yayi, saiki sauke shi, saiki kara yayyafa ruwa sosai tsakin ya jike , daganan saiki zuba gishiri da maggi dai dai gwargwado, sai ki sake maida shi bisa wuta ya yi.
Da ya yi zakiji ya fara kamshi sai ki bude ki dan debo ki ji ya yi taushi idan yayi taushi saiki sauke abinki.
Sai kici da duk miyar4 data birgeki ko maigidanki ko yaranki ko babanki. To shike har mun gama yanzu kuma zamu shiga yadda akeyi na shinkafa
karanta: Yadda ake cake cikin steps masu sauki
Yadda uwar gida zatai fried rice
Abubuwa 12 dake mace tazama tauraruwar girki
yadda ake hada tsire
Yadda uwar gida zatai fried rice
Abubuwa 12 dake mace tazama tauraruwar girki
yadda ake hada tsire
Yadda akeyi burbuckon shinkafa
Uwa gida wannan burabiskon ya abn banta da wance wanda mukayi domin wancen na gero/masara ne wannan kuma na shinkafa ne.
Abubuwanda ake bukata wajen hadawa sune:-
* Shinkafa
* Zogala
* Kayan miya albasa, attarugu alayyahu
* Man gyada
* Gishiri, maggi, kori
Yadda ake hadawa:-
Idan kika gyara shinkafarki, sai ki akai miki nika, sai ki yanka kayan miyarki gabadaya idan kinada ikon sa nama ko kifi in kinaso, saiki zuba gyararren zogalanki aciki. Sai ki yayyafama shinkafarki ruwa ta dan jiku, sai zuba shinkafar acikin madambacin ki ki turara abinki ki bashi wani lokaci, sai ki sauke ki dauko kayan miyar ki da maginki da gishiri da kori. Idan da iko sai asa nama idan kuma hakan bata yuyu ba to babu matsa tunda ba dole bane daman haka eayuwa take in ya kanada shi to gobe bakada shi ko kuma in yau kaine to gobe ba kai bane Alla dai yasa mu dace, Ameen.
Saiki maida tukunyar miyarki akan wuta, da kinji kamshi to ta yi, kafin ki sauke ki tabbata yayi taushi sosai, ko dan kayan haki suyi kamshi. Tabbas yanada dadi ku biyo mu a shiri na gaba ackin wannan website din Hausawa site, idan mutum yanada tambaya ko kuma karin bayani zai iya yi a coment Mungode
Kuma kayi comment ya kayi naka.
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin