Table of Contents
Yadda ake Hada Fried Rice
Assalamu Alaikum jama’a yauma kamar kullum zamu kawo muku yadda akeyin fried rice,
Kamar yadda aka sani dai fried rice hanya ce ta sarrafa shinkafa daga cikin hanyoyin yin girki, saboda shinkafa ana amfani da ita a wajen hanyoyi da dama wajen sarrafata kamar wajen yin sunasur da sauransu, to shiyasa Yana da kyau a ce uwar gida ta iya fried rice dinta Mai dadi sosai don birge Mai gida.
Karanta: yadda ake sunasur
uwar gida ina baki shawara idan kika yima mijinki wannan fried rice din to cewama zai rinka yi kullum ita za’a masa saboda irin dadinta in da yana cin plate guda to yanzu ina gaya miki saima ya ci plate biyu koma ukku ku biyomu domin jin yadda ake sarrafa wannan shinkafar kamar a city.
Karanta: Abincin Hausawa: Ire-Iren Abincin Gargajiya na Hausawa
Abubuwan da ake bukatar uwar gida ta ajiye wajen yin wannan sanwar
Ga lissafin abubuwan da ake bukata wajen hada ta wanda za’a tanada ko a sawo a kasuwa kamara haka:
1. Shinkafa 7. peas
2. Nama 8. Albasa
3. hanta ko koda 9. Attarugu
3. Green beans 10. Maggi
4. Green Peppe 11. Gishiri
5. Carrot 12. kori/ thyme
6. Cabbage 13. Mai
Karanta: YADDA AKE GIRKI COMPLETE SANWA YADDA ZANI GIRKA ABINCI KALA KALA
Yadda ake hadawa
Zaki yanka kayan miyanki kanan, sannan ki tafasa namanki da hantarki kanana ki tafasa ruwan zafi acikin tukunyarki, sai ki wanke shinkafarki ki zuba acikin ruwan zafin, idan shinkafarki tafara alamar dahuwa da garas garas dinta saiki sauke, ki tace, sannan ki dora manki a wuta, idan yayi zafi zaki yanka albasa slice da attarugu kanana, yanxu duka zaki zuba shinkafarki da nama da magi da gishiri da koro/thyme kiyi ta juyawa har sai shinkafarki ta karasa dahuwa duka tare da kayan miyan, idan tayi zakiga tayi wara-wara tayi kyau a fuska, kayan miyan kuma zai fito aciki zakiga yayi shar-shar.
Karanta: Girki Adon Mace: Kala-kalar Girki da yadda zaki kware akan kirki don shine adon mata
yadda ake Spring rolls da meat pie
Amfaninta a Lafiya
Fried rice nada matukar amfani a lafiyar jikin mutum saboda ta kunshi abubuwan da dama da suke kina jiki koma ince ta kunshi dukansu saboda daman ana soin a hada su kuma ta hada.
Daga ciki akwai proteins wanda tya shafi kamar nama, sai kuma vegitables wato vitamins kenan wanda ganyayyaki da ke ke cxiki, ga kuma carbohydrates wanda ita kanata shinkafar da aka zuba a ciki tana da wannan.
Don haka tana da matukar amfani a lafiyar jiki, a riga cinta shiyasa kasashen da suka cigaba suke cin abincin daz suka tabbata yana gina jiki wanda zai kara masu lafiya kuma ya gyara jikin.
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin