Skip to content
Home ┬╗ Yaron da ya samu dala miliyan 22 a internet

Yaron da ya samu dala miliyan 22 a internet

       

       Shidai wannan yaron ba wani yaro bane ba face wanda aka sama suna Ryan wanda zuwa yanzu shekarar sa takwas a duniya, shidai wannan yaron ba wani abu  yake ba da yasamu wadannan zunzurutun kudin ba face yana yin bayani ne a kan kayan wasan yara a wannan sananniyar kafa ta sada zumunta t youtube, a inda ya rinka amfani da shafinsa na youtube wajen yin bayani akan kayan wasan yara wanda hakan ne ya sa ya zama kwani, kuma har ma ya zama na daya a jerin wadanda suka fi kowa samun kudi a youtube.


      A watan yuni ne wannan sananniyar mujallar wadda aka fi sani da forbes ta fitar da sakamakon bincike wanda yake nuna cewar chennel mai suna RyanToysReview ta samu nasarar zama na daya inda ta doke abokiyar gasarta wato Joke Paul da dala kusan dala 500,000 a karshen shekarar da ta gabata.

      A tun lokacinda iyayensa suka bude massa wannan shafin na youtube a shekarar 2015,
bidiyoyin da suka fara dorawa an samu yan kallo wadanda yawansu ya kai biliyan 26, kuma shafin ya samu mabiya wadanda yawan su ta kai 17,300,000, mujallar forbes ta kara tabbatar da cewar kudin da ya samu kusan dala ashirin da daya 21 ya same su ne a sanadiyyar tallar da ake sawa a cikin bidiyoyin da channel din take sawa kuma dala miliyan daya ta hanyar masu daukar nauyinsa.
      
       Duba da la’a kari Ryan karamin yaro ne ba duka kudaden da yake samu ba yake amfani da su ba, ana aje masa kashi 15 ne cikin dari na abunda ya samu a banki kafin ya girma, kuma dudda hakan kudaden da yasamu a bana sun linka wanda ya samu a bara, bayan an cire haraji da kamashon da yake biyan layoyin sa da masu yimasa hidima.
       
     A lokacinda aka zanta da shi a tashar NBC an tambaye shi me yasa ya ke son kallon bidiyoyin sa sai ya ce dalilin shine ya iya nishadantarwa.
      
     suma yan’uwan shi wadanda takwaye biyu ne ba’a barsu a baya ba sun fito a wara bidiyon da yake bayani ga yara yadda ake gudanar da harkar sinadarai na kimiyyar zamani inda suka sami yan kallo wanda yawansu yakai akalla miliyan 26. ku cigaba da kancewa damu a wannan wensite din wato mai taken Hausawasite domin samun post na ilimantarwa, labarai da fadakarwa akan abubuwan dake faruwa a fadin duniya.