Table of Contents
Yadda ake hada Doughnuts
Post din yau yana Magana ne akan yadda ake doughnut mai dadi, inda za mu yi Magana inshallah ko kuma muyi cikaken bayani akan yadda ake hada shi Doughnut din da kuma kayan da ake amfani ko kuma kayan da zaka/ki sawo a kasuwa domin hada wan nan kayataccen doughnut din.
kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda muke koya abubuwa daban daban a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai.
kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda muke koya abubuwa daban daban a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai.
To zamu farad a lissafa kayan kamar yadda aka saba sannan inshallahu mukuma yi maju bayanin yadda ake hada kayan.
Kayan da ake Hada Donut
Filawa
Kawai
Butter
Yeast
Madara
Baking Powder
Flavour
Yadda ake hada kayan Doughtnut din
Dafarko dai zaka/ki jika yeast da ruwa na dumi a cikin rubber ko kuma tasa tsaftatacciya, sai a aje a gefe sannan kuma sai a narka butter a hada da sugar sai ajuya shi ko kuma ince a motsa.
Bayan sugan ya narke sai a zuba rowan yeast akai wanda muka ambata a baya, a zuba baking da gishiri kadan da kuma madara, sannan kuma sai a zuba filawa a kwaba, a kawaba har yay kawri wato kwabin dai ya hade ake so .
Sai a rufe a aje a rana ko kuma wuri mai dumi don kwabin ya tashi , bayan an aje shi ya tashi sai kuma a sake kwabawa a rinka yimasa shape wato circle da huda a tsakiya kamar yadda yawanci aka san shi .
Sai a kara aje shi a cikin rana ko wajen dumi ya tashi. Sai a sa mai a kan wuta yayi zafi sosai ba kuma yadda zai toya shi ba , sannan sai a zuba a cikin kaskon man har yay brown ko kuma dan ja ja haka a kala. Sannan kuma sai a kwashe a zuba ma baki ko kuma mai gida .
Akwai wani post don ki/ka kara kwarewa a harkar girki duba shi wanda shine :Abubuwa 12 dake sa mace tazama taurarwar girki munyi bayani sosai a kansu.
wanda ke da tambaya kar ya ji komai yayi a comment section onshallahu zamu amsa mai a ci dadi lafiya kar a manta dani.
Kammalawa
Kamar yadda muka ga bayani akan yadda ake hada donut to akwai abubuwa wanda ya kamata musamman mata su ringa lura da su kafin ko a lokacin girki wanda shi zai taimaka wajen kara zaman lafiya da kwanciyar hankali a gida.
Misalinsu sun kunshi tsafta, kula da yanayin abubuwan dandano kamar su gishiri share wurin girki da sauransu
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin