Skip to content
Home » Yadda ake connecting din xender a Android da computer a tura files lafiya lau

Yadda ake connecting din xender a Android da computer a tura files lafiya lau

Yadda ake connecting din xender a Android da computer a tura files lafiya lau

Yadda ake tura file daga android ta hanyar connection da computer da xander application ba wani abu bane mai wahala a wannan post din inshallahu zamu yi Magana akan steps din da ake bi don kai connecting din xender application da computer din ka ta hanyar amfani da hotspot.

Yin transfer daga computer din ka zuwa waya ko kuma daga waya zuwa computer yana da amfani musamman ma idan mutum baya da USB cable ko kuma wurin ya lalace a computer din.

Wanda hakan zai sa ka yi amfani da fasahar wireless connection wato wifi da hotspot a tsakanin wayar ka da computer din ka, amma computer din ka ta kasance tana da hotspot driver.



To da farko dai zaka samu ko kuma in ce kayi install din xender a Android din ka in baka da ita ita kuma ana bukatar version mai girma wato na xender app din, sannan kuma ya kasance a computer ka kana da browser kayi download din ta,

 irin su ChromeFirefoxOpera, internet explorer da ma sauransu in baka da su danna sunan su kai download  to ya kasance dai akwai koda day ace kayi install a computer dinka.

To idan ka tattara wadannan abubuwa shikenan sai ka bi steps ko matakan da zamu ambata a post din nan Inshallahu.


             

Mataki na Daya:

Za ka/ki shiga xender a cikin android din ka

Mataki na biyu:

Zaka daanna daga sama gefen hannun hagu



Mataki na ukku

Zaka ga option sai ka danna connect to pc


Mataki na biyar sai ka danna hotspot


Mataki na shidda : sai ka danna create hotspot zaka gay a nuna ma ip address kammar haka
Idan yayi haka acikin computer din ka zaka ga abun nuna service sai ka danna shi kai connect


Mataki na bakwai: sai ka shiga a cikin browser ta computer din ka, sai ka rubuta ip address din da xender ta nuna maka a can saman inda Ake rubuta website address.
Mataki na takwas:

Bayan ka rubuta ip address din da wayar ka ta nuna maka a browser din computer din ka sai zaka ga a cikin android dinka akwai notification yasa “connect to pc ” kamar foton kasa sai ka danna accept


To da kayi wannan shikenan idan ka zabi foto ka danna alamun download a cikin computer zakaga ya sauka a ciki  idan upload ka danna zaka ganshi a wayarka.

Idan ka sauko ko kuma ka tura daga wayar ka zuwa computer to a computer zaka duba folder wadda ake cema Downloads nan zaka samu abubuwan da ka turo.

To Alhamdulillah ga mai tambaya ko Karin bayani yana iya yi a comment section wanda ke a kasa.