Skip to content
Home » Yadda ake hada yam Ball a cikin steps masu saukin yi

Yadda ake hada yam Ball a cikin steps masu saukin yi

Yam ball image


Yadda ake hada yam Ball a cikin steps masu saukin yiA wannan post din zani yi Magana ne a kan yadda ake hada yam ball a cikin steps masu sauki wato a cikin hanya mai saukin yi, to kamar yadda dai kowa ya sani shi yam ball ana hada shi ne doya sannan kuma a hada wato ita doyar da sauran kayayyaki wadda zasu kara mata armashi kuma abinci ne wanda aka saba dashi kusan mafi yawancin mutane suna cin sa bama a kasar hausa ba a kusan fadinduniya gabakiya.

Ýam ball dai kamar yadda kowa ya sani abinci ne wanda yake hade da sinadaran da jiki domin yana kunshe da sinadarai irin su protein wanda suke kara gina jiki  a sanadiyar a cikin kayan hadin akwai irin su nama da kwai,da kuma sinarai na starch wato daga ita kanta doyar.

To kamar yadda na saba a cikin wannan website din ta Hausawa Site muna koya yadda ake hada abubuwa kala kala cikin su hadda abinci kamar Yadda ake hada Alkaki kuma a kowane post ina fara zaayyana kayayyakin da ake amfani das u sannan sai kuma muje zuwa yadda ake hada wagto su kayan gabakidaya.

To inshallahu ma a wannan ma haka zamu yi da farko zamu fara lissafa kayan da ake bukata don hada yam ball sannan mu je zuwa yadda ake hada kayan da ake hada yam ball din.

Kayan da ake hada yam ball da su


Kayan da zamu lissafa  a kasa sune ake hada yam ball da su wadda zaa nemo ko kuma a sawo a kasuwa wanda basu da wahalar samu.

  1. ·        Doya
  2. ·        Kwai
  3. ·        Albasa
  4. ·        Attarugu
  5. ·        Magi/gishiri
  6. ·        Nama
  7. ·        Mai

Matakan ko steps din da ake bi wajen hada kayan yam ball din

To dafarko dai zaa fere doya mai kyau sannan sai a sa ruwa a wanke ta sosai sai a sa  ta a cikin tukunya a dafa idan ana da bukatar gishiri ana iya sawa kadan a wajen dafuwar bayan ta dafu sai a sauke tukunyar sai a tace ita doyar sai ki aje a wuri daban.
Daga nan kuma sai a yayyanka albasa da attarugu a zuba a turmi a daka ko a kirba, sannan sai a zuba magi da gishiri dan kadan a cikin turmin a cigaba da dakawa.
Sannan sai a debo dafaffar doya a daka ana dakawa sama sama sannan a juye a cikin kwano sannan a dauko nama sai a zuba shi a kai.

Idan  ana so kamar gishiri bai ji ba  sai a kara yadda zai daidai ta sai a juyasu a dunga mulmulawa  ana tsomawa a cikin rowan kwai sai a dora kaskon mai yayi zafi sai a cigaba da soyawa har ya soyu  daga nan kuma sai a kwashe a zuba a cikin kulak o kuma kwano.
To daga nan ne muka kawo karshen wanan post din na yadda ake hada yam ball a cikin steps masau sauki wanda ko wacce keda tambaya ko Karin bayani akwai comment section sai a yi kuma ana iya koyan yadda ake meat pie da yadda ake sprong rolls suma munyi basyanin su.

Mungode.