Tarihin bayajidda zamu yi magana a cikin wannan post din na wannan website din tato hausawasite. Kamar yadda kowa ya sani tarihin bayajidda daddaden tarihi ne wanda ake yi shi da dadewa kuma kuma yana daya daga cikin jigo na tarihin asalin hausa inda wasu ma kusan suna cewar shine kusan asalin hausa. Akwai littatafan hausa awannan website don yin downloading kamar Download Ruwanbagaja pdf, na hausa da ma na Larabci
Table of Contents
TARIHIN BAYAJIDDA Tarihin Asalin Hausa Na Bayajidda Gamsashe
To kamar yadda ake ta cece kuce game da tarihin bayajidda wasu na cewa dagaske ne shine asalin hausa wasu kuma suna cewar a’a To amma kai mai karatu mi kake gani shiun shine asalin hausa koko? Kuma da a yadda tarihin bayajidda ya nuna cewar yazo a daura to da yazo a daura shin su wane irin yare suke yi a wancen zamanin?
Waddannan duk kusan wasu tambayoyi ne da yakamata mai karatu yayi ma kansa kuma
idan akwai amsa kana iya yi a comment section ko sation yin comment a wannan website din.
Tarihin bayajidda Kafin zuwa Garin Daura da lokacin da yazo Daura
To kamar dai yadda tarihin ya nuna cewar asalin sunan Bayajidda abu yazid dalilin ma
da yasa a ka sa masa baya jidda shine da bay jin maganar hausa daga kalmar baya ji.
Shidai bayajidda mutum ne jarumi wanda kusan kamar yadda tarihi ya nuna cewar ya taso ne daga kasar Bagdad wato kasar bagadaza a hausance inda yake ta tafiya har iso a
garin Borno wato a karon farko. A inda daga bisani kafin ya baro garin Borno Akwai
dalilan da suka sa haka Sune a cen garin Borno sakin Borno na lokacin ko a ce Mai ya aura ma shi Bayajidda diyarsa a inda daga nan suna zaune ya samu rade radin cewar
sarkin zai kashe shi. Daga nan bayan sun samu labarin haka sai matarsa ta umarcesa
da su gudu su bar garin inda daga nan suka kama hanyarsu har zuwa kasar hausa.
Wani sashen na masu tari yana nuna cewa a tarihin bayajidda ya taso ne yana ta tafiya har sai da yazo a garin daura ya sauka a garin da daddare a cikin gidan wata mata tsohuwa
Kashe Macijiya
A yayin da ya sauka a lokacin yana jin tsananin kishirwa inda ya tambayi tsohuwar nan da ya iske ta bashi ruwa ko kuma ina rijiya take yaje ya debo ruwa don sha sai tace masa
ay su basu dibar ruwa da daddare a sanadiyyar sarki wato shi wani katon maciji ne dake hana mutanen garin dibar ruwa daddare.
Daga nan fa ne sai bayajidda ya nufi wannan rijiya ba tare da razana ba inda yaje zai
debo ruwa sai macijin nan ya yo kansa da niyyar hana sa to fa daga nan ne ya fiddo takobinsa ya sare kan sa.
To a lokacin da ya sare macijin nan ya manta waren takalminsa a bakin rijiyar. A lokacinda gari ya waye sai mutanen da ke cikin gari suka zo dibar ruwa a inda suka tadda macijin
nan kansa a sare sai suka kama murana tunda yanzu ba wani abunda zai hana su
dibar ruwa a wannan rijiyar kuma suka tarar da takalminsa ware da kuma kan wannan maciji.
Karanta:
Bayan Bayajidda ya kashe Maciji
Mutane suka taru a fadar sarauniya daurama wadda ke mulki a kasar daura suna ta
murna inda suka shaida mata cewar an kashe wannan maciji amma ba’a san waye ba amma
fa wanda ya kashe wannan maciji ya bar rabin takalminsa a gindin wannan rijiya.
Daga nan fa ne sarauniya ta saka babbar kyauta inda tace ta yi alkawarin zata auri wanda ya kashe wannan maciji kuma zata basa rabin gari amma azo da waren takalmi domin tantance wanda yayi abun.
Ana cikin wannan yanayi dai kwatsam sai ga wannnan tsohuwa a inda tazo ta ce ta san wanda ya kashe wannan maciji.
To daga nan ne ta kwashe labarin abinda ya faru sai sarauniya ta auri bayajidda kuma
ta basa rabin gari.
Karanta:
Takaitaccen Bayani Game da Garin Daura
Kamar yadda mai karatu ya lura zai fahimci a cikin bada tarihin bayajidda ana ambatar wani gari Wanda ake cema Daura to shi Garin Daura back wani gari bane face Daya daga cikin gundumomi na Garin katsina wato local government a turance Wanda ya dade da dumbin tarihi Kamar dai irin wanna na baya jidda Kuma har yanzu sarki ne take mulkarsu ba hakimi ba.
A Karshe
To mai karatu wannan shine tarihin bayajidda na kasar hausa wanda masana tarihi kusan suna alakanta shi da asalin hausa da kuma alummar hausawa musamman ma na kasar
Nigeria. Muna fatar mai karatu idan yana da tambaya ko kuma wani karin bayani yayi shi a wajen tsokaci na wannan website din wato comment section don duba wasu daga cikin rubutunmu kamar yadda ake login Email address a waya sai a duba don Karin ilimi
Hausa Bakwai da Banza Bakawai
Akwai garuruwan da aka raba su zauawa abunda ake kira da Hausa Bakwai akwai kuma wanda ake kira da Banza Bakwai., garuruwan da ake kira da hausa bakwai ga su kamar haka.
- Daura
- Katsina
- Kano
- Zazzau
- Gobir
- Rano
- Biram
Sai kuma a dayan bangaren wadanda ake kiransu da banza bakwai sun kusni
- kebbi
- zamfara
- yawuri
- gwari
- nupe
- kororofa(jukum)
- illorin
Karanta:
Yadda Zaka samu kudi da abubuwan da ka iya da Computer su zama Sana’arka da inda zaka koye su
Cryptocurrency da yadda ake samun kudi da shi
Minene Bitcoin? Cryptocurencies da Abubuwan da ya kamata ka fahimta game da su
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin