Skip to content
Home » Yadda ake Bude Email Address a waya ko Kuma a Computer – Bude Gmail Account ko Kuma Bude Email Address a cikin steps masu sauki

Yadda ake Bude Email Address a waya ko Kuma a Computer – Bude Gmail Account ko Kuma Bude Email Address a cikin steps masu sauki

       Tabbas bude Email Yana da amfani sosai musamman ma ta yadda zamani ya cigaba, a cikin wannan post din zamu Yi magana akan yadda zaka bude email address dinka a cikin wayarka ko Kuma computer din ka .

 

Karanta: Yadda zaka bude website

Yadda ake login Email address

   
Bude Email

 

  Kuma Ina son Mai karatu ya fahimci cewar kana iya bude email din da zamu Yi bayani a wayar Android din ka ko Kuma computer din ka Kuma Kai logging kamar Facebook account din ka
  Amma kafin mu tafi zuwa taken post din nan bari mu Dan Yi tsokaci akan email address.

Menene Email address ko Kuma account Kuma kala nawa ne?

      To shidai Email Address ba komai bane ba face adreshin tura sako ta hanyar fasahar yanar gizo  Wanda kamfanunuka da dama na bude shi irin su  Google  Wanda ake Kira da Gmail da kamfanin Yahoo Wanda Suma suna bude Yahoo mail.
       Wadannan kamfanunuka Basu kenan ba akwai da da dama Amma anfi saninsu don sun fi Shahara a duniya.

Amfanin Mallakarsa

A duniyar yanzu Email yana da matukar amfani kuma rashinsa illace ga mutum saboda yanzu tun daga jarabawa kamar irinu Jamab ana bukatarsa kuma yana da kyau ace kai kanka ka san yadda zaka bude ma kanka ba dole sai kaje wajen wani ya bude maka ba.

Amafanin email ga kowane mutum

Ga wasu daga cikin muhimman amfaninsa kamar haka a zayyane.

  • Aje lambobin waya bayan cikar layin waya
  • Adana hotuna da abubuwan waya musamman a halin da ake bukatar rabuwa da ita
  • Cike Ayyukan a online
  • Fannin jarabawa da makaranta dole sai da shi
  • Samun bayanai tura sako da kuma amsar sakonni.

 Wadanne abubuwa ne Nike buka kafin in bude Email?

      To abubuwan da kake bukata gasu kamar haka zan lissafa su a kasa.
1. Suna da Kuma sunan mahaifi
2. Ranar haihuwa wato sanin date din haihuwa.
3. Waya ko computer
4.lambar waya
5. Cikaken adreshi.

 

DUBA WANNAN: Yadda ake Download din YouTube videos a computer cikin steps masu sauki                           Yadda ake maida page din website ya zama pdf a computer ko a waya.            yadda ake hada tsire            yadda ake samosa             Download Ruwanbagaja pdf             yadda ake hada yam-ball ita             how to easily connect xender to android             yadda ake connecting din xender da android.             yadda ake hada yamball             yadda ake fried rice              yadda ake spring rolls da meat pie                yadda ake yin pizza                     yadda ake hada samosa
Download littafin Ruwanbagaja pdf

 

 

    Matakan Da zaka bi wato don bude email address dinka na Gmail.

Form Na Email

 

 

 

 

 

Dafarko dai ka je address din accounts.google.com sai  cike form din da suka baka na farko zaka cike sunan ka sai Kuma ka cike na mahaifinka.

  Daga nan Kuma sai ka zabi sunan da yayi ma Wanda zasu sama misali suna@gmail.com kasani ka kirkiro naka sabon suna Wanda ba Mai irn shi

   Daga nan Kuma sai ka rubuta password din da kake so kayi amfani da shi Mai wahala zaka sa takai kalma 8 haka.

   Daga nan Kuma sai ka rubuta lambar wayar da kake so ka bude email da it’s Wanda take kusa da Kai don said kayi varfying din ta

   Daga nan Kuma sai ka rubuta ranakun haihuwarka wata da shekara da Rana.
   Daka Yi haka sai ka Danna mabalin Next ka you agree na trms na Google
Daga haka Kai Yi ta sa next shikenan ka gama

Gararabasar da Masu Gmail Suke Samu

Kamar yadda a post na kawo wasu daga cikin Apps Suke da Amfani a rayuwar yau da kullun, kamfanin Google ya bada wasu Apps a matsayin garabasa Kyauta ga wadanda suke da Gmail Account ba kamar wanda suka bude da Yahoo ko Hotmail ba.
Gmail Account

 

Daga cikin wadannan apps din sun hada da Google photos shi wani app ne wanda zaka iya aje hotunaka saboda tsaro, misali halin rayuwa wayar ta bace ko a sace.
Akwai kuma Drive wanda ake dora abubuwa ko files a cikinsa kamar yadda a post na koya yadda ake aje abubuwa a Drive don gudun salwantar su, kuma zaka iya tura ma wani ma yaga abunda ka aje har ma in yana so yayi Download.

Kaga yana da matukar amfani saboda wajen ajiya ne kusan na har abada saboda a server zaka dora su koda yaushe kake so zaka iya samunsu.

Kammalawa

Email address dai adreshi ne na yanar gizo wanada yake baka dama ta tura sakonni ko Kuma amsa su a sassa daban daban na fadin duniya domin sawwake sadarwa.

Baccin ka Bude shi Kuma kana iya login ka cigaba da amfani da shi a wayar ka ko computer inda shima mun koya shi karata yadda ake login Email address a waya da Kuma Yadda Ake Tura Sakon Email address  domin Karin haske, Wanda ke da tambaya yayi a comment section a kasa.