Skip to content
Home » Yadda zaka bude karamar website na Blogger | Lesson 1

Yadda zaka bude karamar website na Blogger | Lesson 1


    yadda ake bude website kenan ka zo ka kowa danuwa da kyau haka ne to a wannan post din maganar da zamuyi shine yadda ake hada website ,Tabbas website tana da amfani sasai musamman wajen bunkasa kasuwanci saboda ita wata aba ce wadda in aka bude ta kowa zai iya kamawa ko ya shigeta a fadin duniya ta hanyar address dinta a yau inshallahu zamu yi magana ne akan yadda zaka hada website din ka karama ta blogger wadda ba sai ka kashe kudi ba.

      Nazari kafin Bude website


     Kuma ita website akai ma abubuwan da ya kamata mutum ya tsaya ya sani natsu ko Kuma ince yayi planning kafin ya fara ta saboda in ka fara ta akwai aikace aikace da dama da zaka yi akanta.
  
   Domin akwai tsare tsaren da sai ka tsaya kayi nazari akan su kafin ka bude website din domin hakan ne zai taimaka ma wajan juriya da Kuma son bunkasa ta a koda yaushe ba tare da gajiyawa ba.

    Wanda shiyasa na sa hoto Mai hade da bayani Wanda mutum zai iya dubawa don gani abun a kasa.

Yadda zaka bude karamar website na Blogger

Blogger mallakar kamfanin google ne wanda zaka iya amfani da shi don bude website  wnda idan ka bude zakaga address din website din a misalin www.sunanwebsite.blogspot.com .
 A baya nayi magana akan akan yadda zaka aje photo na wayarka har abada ko wayar ta bata in baka karanta shi ba duba.

Yadda ake planning website kafin a hada ko a bude

A baya mutum bay iya bude website da kanshi in ba yana da ilimin programming language ba ko kuma ya samu wanda ya iya ya biya sa kudi ya bude masa amma yanzu cikin ikon Allah ta sanadiyyar bunkasar technology wato kimiyya da fasa akwai hanyoyi daban daban da zaka iya bude website dinka kuma ka rinka yin post lafiya ta rubutu kamar yadda ka keyi da a facebook dinka.

Matakan da zaka bi Don ka bude blogger website

Dafarko dai kafin komai sharadi na farko shine ya kasance kana da gmail account wato email na kamfanin Google in baka da shi danna don ka bude Bayan ka bude kana iya login. din Email din a cikin wayar ka  

1. Da farko zakaje website din  Blogger 


2. zaka shiga kayi sign in in baka manta ba a baya mun yi maganar sai kana da gmail account to shi zaka sa ka sa password din ka kuma.


                         yadda ake connecting din xender da android.
                         yadda ake tsire
                         yadda ake hada yamball
                         yadda ake fried rice 
                         yadda ake spring rolls da meat pie   

                         yadda ake yin pizza  


3. Sai ka danna continue to blogger kuma bayan ka danna sai ka sa danna create new blog.
4. T o bayan ka danna create new blog zai bude ma wata kofa sai ka sa tittle wato taken website din ka wadda zaka sa. Idan ka duba zakaga a nawa nasa masa misalin hausawasite to a nan sunan website din ka zaka rubuta.


5. Daga nan kuma a kasa da wannan zaka ga ansa wajen addres sai ka sa sunnan website tittle dinka a dunkule da .blogspot.com misalin yadda nasa nawa misalinhausawasite.blogspot.com. kamar haka.
in yayi dai dai zakaga good bla ya fito, kuma ka zabi template din website din.


6. Daga nan kuma sai ka sa create blog kamar yadda wannan hoton ya nuna. To barka ka bude website din ka na farko a sauran gyarata da samata abubuwa masu amfani.

7. Daga nan kuma zaka iya shiga dashboard wato wajen da ake sarrafa website din don yin abubuwa daban daban miasalin in zaka yi post sabo zaka danna new post a wajen dashboad din ka kamar haka.

   To a wannan mataki ka kammala hada hada website din ka blogger yanzu abinda ya rage ma shine postin da samun traffik wato masu shiga a cikin website din zamu cigaba da koyawa a nan gaba inshallahu yadda zaka ida yin kingin abubuwana wanda keda tambaya yana iya yi a kasa wajen commen section zan duba in amsa masa inshallahu kuma zan kara post sosai ba da dadewa ba na koyarwa sai kadawo karanta su. To fa kai ya ka hada.