Skip to content
Home » Yadda ake hada man shafawa verseline

Yadda ake hada man shafawa verseline

Yadda ake hada man shafawa verseline

     Man shafawa abu ne wanda kusan kowa yana amfani da shi domin shafawa a jiki domin yin kwalliya ko kuma domin kyaran fata domin kare ta daga bushewa ko tsagewa.

   A yau inshallahu zamu yi magana kon kuma zamu koya yadda ake hada man shafawa a cikin steps ko kuma matakai masu saukin yi, wanada in ka bi su zaka hada mai mai inganci wanda har ma saida     shi ana iya yi a kasuwa domin a samu kudi. A baya mun taba yin magana akan  yadda ake hada air freshner to yau kuma inshallahu mai na shafawa zamu yi magana akai

Shin ana samun kudi da man shafawa kuma a ina zan saida shi?

Tabbas ana samun kudi da man shafawa kiamar su sabulun wanki ne shima musamman in aka gyara kasuwancin aka yi mai inganci wanda ba hainci a cikin sa to zaka ga yayi kasuwa sosai kuma mutane na saye, wasu ma mutanen kusan har abun dogaro da kai suke samu a sanadiyyar sanaar man shafawa.
     
sai dai ya kamata mai karatu ya san cewa a kowane irin kasuwanci yana bukatar yin abu mai sauki wanda zai dadawa costomomi.

    Manyan kamfanoni dasuka samu kudi ta sana’ar man shafawa.

    Sanin kowa ne ko a kasarmu ta nijeri ko Kuma ga wadanda suke a cikin nijer tabbas akwai kamfanunnuka wadanda muna son shafa man su.
          A dalilin cewa man su na da inganci shiyasa Kuma suka samu kostomomi masu yawa.
   To kaima Mai karatu in ka kyara hakane zaka samu da yardar Allah misali yanzu fresir Mai ne na shafawa Wanda kusan kowa a Nigeria yasan shi saboda mi kowa yasan man Nan Yana da kamshi ga kyau Kuma to idan zaka hada Abu yi Mai inganci ka kyara kaima zaka samu.
 

Yadda ake hada man shafawa

To ba tare da bata lokaci ba sosai ba bari mushiga a cikin post din sinadarai ko chemicals din da zaa sawo ko a nemo wanda ake hada man shafawa dasu.

Post Din yadda Ake fara kasuwancin saida man shafawa

   Akwai post Wanda muka rubuta Wanda yayi magana akan yadda zaka fara kasuwancin saida man shafawa inda jerin sinadaran da tsokaci a kan su mun Yi magana kana iya duba shi shima.

Karanta
Yadda Ake fara kasuwancin saida man shafawa Verseline

Sinadarai ko chemicals din da ake hada man shafawa verselin dasu

  1. Tuwon mai ( ko a turance petrolleum jelly)
  2. Ruwan mai.
  3. wax 
  4. Turare ( mai kamshi yadda ake so).
To wadannan sinadarai sune ake hadawa da na ambata abaya sune sinadaran ko kayan hadina man shafawa wanda zaka iya saya a kasuwa ko kuma idan karasa inda zaka samu kayan hadin kana iya yiman magana a comment section a kasa ko kuma ka kira wannan numbar  waya +2349037157675 

ko kuma ka tura mani da sako ta e-mail a 

fasahaltd@gmail.com .duka kana iya amfani dasu ka kirani in zaka saya sai kasaya a wurina inda bukatar hakan,idan a nigeria kake a arewacinta zanyi kokari aturama kayanka har gida. 
                     KARANTA:   how to easily connect xender to android

                         yadda ake connecting din xender da android.
                         yadda ake tsire
                         yadda ake hada yamball
                         yadda ake fried rice 
                         yadda ake spring rolls da meat pie   

                         yadda ake yin pizza  

                        Yadda Zaka Aje Photon Wayar Ka Na Memory Har Abada Ko Ba Wayar                                                                                                                                                     yadda ake hadin sinadaran ko chemicals din man shafawa ko vaseline.                                            

  1. A mataki na farko dai zaka samu tukunya mai tsafta ka zuba kamar awon kilo daya na tuwon mai wato petroleun jelly a cikin tsaftatacciyar tukunya.
  2. Dauko ruwan mai ka zuba shi acikin tukunyar shima kamar yawan kusan roba ta lemu daya .
  3. Daga nan kuma sai ka balli wax wato kamar yawan tafin hannu daya ka zuba a cikin tunyar.
  4. Daura tukunyar a saman murhu ko wuta madaidaiciya ka dafa su har sai sun narke soasai.
  5. Bayan sun gama narkewa sai ka zuba turare a ciki yadda kake so yayi kamshi,
  6. Daga nan bayan sun narke sai ka dauko robobi ko wurin da zaka zuba man ka, sai ka samu waje mai sanyi ka aje shi ya huce har tsawon awa biyu ko awa ukku, bayan ya narke zakaga ya koma man shafawa lafiyayye inshallahu.
kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai  Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu

man shafawa(verselene)


A Karshe 

Yanayin hadin in kaje kasuwa ake hada ma in kaje wajen masu chemicals a cikin kasuwa ya danganta kilo nawa ne kak so a hada maka zasu hada ma. ko ka tuntubeni in kana so a hada maka ta waddannan address din da ke a kasa.

Email address
fasahaltd@gmail.com
+2349037157675
ko a facebook a www.facebook.com/Hausawasite


To ga masu tambaya kar su damu su yi a wajen comment section a cikin wannan website din, to fa kai ya kayi !!!