Skip to content
Home ┬╗ Yadda ake sa Hoto a cikin Rubutu (Post) din Blogger

Yadda ake sa Hoto a cikin Rubutu (Post) din Blogger

 

   Yadda ake sa Hoto a cikin Rubutu Post din Blogger

    Yana da kyau mutum ya say hoto a Rubutun post din da yayi a blog din shi domin hoto  kusan shi ke fiddo kyawun website ko blog din mutum Wanda shiyasa zamu koya yadda zaka sa hoto a cikin post din ka na blogger.

Hoton blogger

         A baya dai mun Yi magana akan yadda ake bude blog inda mukai bayani dalla dalla kan yadda zaka bude blog dinka Kuma muka Yi bayani akan yadda ake Rubuta post a blogger in baka iya ba sai ka duba ka karanta bayanin da muka Yi.
 
       To shiyasa yau zamu Yi bayani akan yadda ake sa hoto a website na blogger
Duba ga yadda hoto ke da amfani a cikin post Wanda Yana taimakawa sosai ma fanin SEO watau saurin indexing a Google.

      Minene mahimmancin sa hoto a cikin post?

      Tabbas sa hoto na da mahimmanci sosai ma saboda kusan shi ke fiddo website din mutum sosai
   
      Kuma Yana Kara dankon zumunci tsakanin Kai da ma su ziyartar blog din ka ko website dinka.

     Kuma daga cikin babban mahimmanci na sa hoto a website shine don Karin SEO watau (sengine optimization) a turance kenan.

   Domin Google suna ba website masu sa hoto mahimmanci sosai a wajen bada amsa.

  To tunda munga mahimmanci shi bari muga matakan da ake sa hoton a cikin. Post.

  Matakan Da ake Bi Don said Hoto a Blogger.

     Da farko dai ka shiga a dashboard din blogger baka

 

Hoton yadda ake said sabon hoto
Sai ka Danna Danna new post don hada post ko Kuma ka sa Edit post ka Yi editing din shi.
Daga nan Kuma bayan ka shiga idan da farko zaka sa hoto sai ka Danna alamar hoto dake hannun dama
Abun da hoto a blogger
Bayan ka Danna zaka ga ya nuna maka wata kofa inda zaka ka ya nuna ma upload sai ka Danna in daga wayarka zaka sa hoton.
Sa hoto ko upload din hoto
Daga nan Kuma sai ka  ga ya bude ma wajen folder sai ka zabi inda ka aje hoton a wayar ka ko computer din ka.

Jerin folder

Daga nan Kuma bayan ka zabi hoton ka Yi  upload zakaga ya bude kamar haka.

Yadda ake said properties na hoto
Bayan ka Danna hoton ya fito sai ka Dan Danna shi wato kayi highlight din shi zakaga ya nuna ma properties sai ka sa properties din shi   sunan hoton  da Karin bayani.

yadda ake bude Email address 

       Kammalawa

   To kamar yadda kuka gani a wannan post din mun Yi bayani akan yadda zaka sa hoto a blogger dinka Kuma muna fatan duk Wanda keda wata tambaya ko Karin bayani Yana iya Yi a comment section.