Skip to content
Home » Yadda ake Samun kudi ta hanyar amfani da Internet a wayarka ko kuma a cikin computer din ka don bunkasar Kasuwanci

Yadda ake Samun kudi ta hanyar amfani da Internet a wayarka ko kuma a cikin computer din ka don bunkasar Kasuwanci

      Yadda ake samun kudi tabbas wani abu ne wanda kowa yana son ya sanshi musamman ma matasa kuma ba wai karan hanyoyin bane a’a akwai hanyoyi da dama wada ake binsu don a samu kudi muasamman ma zuwan cigaban kimiyya da fasaha na yanar gizo watau onternet. Shiyasa a wannan post din zamu koama yadda zaka samu kudi sposai ta hanyar amfani da wayar ka ko kuma computer dinka. Duba yadda zaka samu kautar kudi a Let’s chat App kafin su gama program din munyi bayani shima

Yadda are samun kudi da waya ko a computer
      To kamar dai yadda muka yi matashiya a sama hanyoyin da ake samun kudi suna da yawa kuma zamu raba su dala dala don mai karatu ya fahimta sosai.
Kuma kafin mu yi bayani akan yadda zaka samu kudin a kowace hanya zamu lissafa su a karon farko tukunna kanan muje zuwa bayaninsu filla filla. Amma zamu dan tsokaci kan gasuwanci kafin mu lissa fa su.
Karanta:
 

Tsokaci Game da Samun Kudi ko kuma Kasuwanci Bakidaya

Amma bari dai mu dan yi tsokaci kadan game da kasuwanci ko kuma samun kudi.
Dole ya kamata mai karatu ya fahimci cewar kafin ka samu ku7di a duniyar nan fa sai ka shiga a cikin rayuwar wani.
Idan na ce haka nasan mai karatu zai so ya gane mi nike nufi to ka shiga rayuwar wani yana nufin ka taimakawa wani dole sai ka taimakawa wani ka fidda mai lalurar shi ne sanan kaima lalular ka zata fita wato kasamu abin hanun shi.
Misali mai saida abinci dole sai da ta tanadar da abunda zata taimakawa mutane da yawa kanan take samun kudi in ba wanda yaji yunwa kaga ba mai saye kenan.
Wani ma misalin shine Dangote Yafi kowa kudi a cikin afrika to ka duba mutum nawa yake taimakamawa daga ma’akata har zuwa kostomomi. To kaima dole in ka fara kasuwanci ka tabbatar da kayi abu na gari wanda zai taimakawa al’umma kuma ka ba abin lokaci da hakyri don komai sai ahankali yake tafiya.  Akwai wani labari akan yadda wani yaro ya samu kudi a internet

Hanyoyin da ake samun Kudi da su ta hanyar amfani da waya ko kuma computer

   

Samun kudi a internet a ways ko computer

 

 

 

       Akwai hanyoyi da dama da zaka ribantu da wayar ka ko kuma computer din ka musamman in kana da waya mai inganci mun yi bayani akan  yadda zaka sayi wayar android mai inganci a baya kana iya duba shi
  1. Ta hanyar bude Website
  2. Ta hanyar Android Applicxation
  3. Ta hanyar saida data
  4. Ta hanyar saida kati ga jama’a
  5. Ta hanyar Bude Online Store a Shafin sada zumunta irin su (facebook)
  6. Bude YouTube Channel

To Tunda Mun lissafa Hanyoyin da Zaka samu Kudi ta Hanyar Wyar ka ko kuma Computer bari mu tafi zuwa bayanin su

kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai  Domin kasancewa damu kana    iya    Rubuta   Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu

1.  Bude Website:

    Tabbas ana samun kudi ta hanyar bude website musamman ma in kana da mutane da yawa wandi suke ziyartar website dein kamar wannan website din mutane da dama suna Ziyar ta ta kowa ce rana kusan Dubunnan mutane suna shigowa a duk wata na duniya wanda a dalilin haka muka bude wani shiri na taimakwa yan Kasuwa domin bunkasa kasuwancinsu ta hanyar yi masu tallata hajarsu.To kaima kana iya bude website ko karama ce in kana so ka bude ka duba post din mu akan  yadda ake hada website karama mun koya shi a wannan website din.

2.   Hada Android Applications.

     Tabbas ana samun kudi ta hanyar hada android application din ka musamman ma idan ka da ilimi da kuma kwarewa a wajen fanin na’ura mai kwakwalwa, duda dai cewar yanzu a wannan zamanin ba wai sai dole mai ilimin computer ne kadai ke iya hada android application ba.
  Kusan kowa yana iya hada shi idan yaje irin su websites kamar su andromo, appy pie da kuma websites irin su thunkable.
     To yadda ake samun kudi ta fanin hada android application shine kodai ka sa tallace tallace wanda duk idan wanda ke amfani da internet ya yi amfani da application din a wayarsa da data a bude zai ga talla idan ya danna to zaka samu kudi.
   Wadannan irin su sune Google admob kamfanin Google da ke biyan masu publishing da talla na kamfanin google.
   Wata kuma hanyar wadda ita ce gaskiya tafi itace ta hanyar saida kaya a cikin app din ka wanda in kanada install sisai zaka ga kana samun kudi sosai.
   Kuma dai akwai wata hanyar wadda ake cema subscription wato ita wannan hanyar za’a yi subscrib akan wani aiki dakesaidawa a cikin app din ka.

3. Samun kudi ta hanyar saida Data

   Sana’ar saida data ana samun kudi sosai musamman idan mutun yana da hakuri da juriya da kuma maida hankali akan kasuwancin domin ita data kusan mutane da yawa suna amfani da ita.
  Shi yadda kasuwancin data yake shine zaka sawo daga mai rabawa ya saida maka a farashi mai sauki inda kai kuma zaka samu costomin ka ka saida masu, wanda har a wayar ka kana iya saidawa don ka samu kudi
  Kana iya samun kudi ta hanyar internet a wayarka ta sana’ar saida data kamar misali ka bude Facebook page whattsapp group din ka dama sauran kafafen sada zumunta da muke dasu daban daban.

4. Saida kati ga jama’a

Musamman a wannan zamanin kusan kowa yana da waya kuma dole ma ne kowa yayi kira ko kuma tura sako da wannan wayar to ka ga dole kuma kafin a aywatar da wadannan abubuwan sai da kati na waya kanan, shiyasa saida kati abu ne ko kuma sana’a ce wadda kusan tana da kostomomi sosai idan mutum yayi hakuri.
   Saida kati kusan hanya biyu ce akwai printing wato buga kati kana iya sawo kati ka rinka yin printing don saidawa ga masu sari.
  Akwai kuma dayar hanyar wato itace ka saro ka rinka saidama masu bukata na day daya duk lafiya lau.
   To ko a wajen sayda kati shima kamar data ne domin kana iya turawa ga wanda ya sa koda a ce ba kusa da kai yake ba ta hanyar amfani da internet.
Misali ka bude group din ka na whatsapp kuna iya yin magana da wani wanda zai saya a ciki daga nan kai yayi ma transfer na kudi a account naka kai kuma ka tura mashi katin zuwa lamabar wayar shi.

5. Saida kayan Sana’a a shafukan sada zumunta

   Kana iya samun kuda da wayarka ko kuma a computer din ka ta hanyar saida kayan amfani na yau da kullun ga mutane musamman a kafafen sada zumunta irin su facebook,instagram da sauransu.
Saboda internet waje ne da yatara mutane da dama kawai abunda ya rage maka babba kuma shine mai wahalar tara followers, domin da followers zaka iya samun kostomomi da dama wanda zasu rinka sayen kayanka kana iya saida irinsu shadda hula da ma sauransu.

6. Bude YouTube Channel

Bude YouTube channel na daya daga cikin muhimman hanyoyin zamani da ake samun kudi da su kamar yadda mukayi bayani a post din hanyoyin samun kudi da youtube channel.

Samun kudi ta youtube

Wannan ya zo ne sanadiyyar yanda mutane suke yawan so su kalli bidiyoyi a wannan zamani wanda kuma shi ne abunda ya ja YouTube ya kasance manemar internet ta biyu wadda mutanen duniya suka fi bincika bayan Google.

Wannan hanya dai ita akwai hanyoyi da dama da zaka iya samu da su kamar ta hanyar sa talla da program da Google adsense ko kuma ta hanayr saida hajarka, ko kuma ta hanyar baka talla daga waje.

Wadannan sune manyan hanyoyin da ake samun kudi da su a kafar sada zumunta ta youtube wanda idan mutum ya dage yana iya ma samun na rayuwa sosai

Karanta: Yadda ake bude YouTube Channel

Kammalawa

 To kamar dai yadda mai karatu ya karanta mun yi bayani sosai akan yadda zaka yi amfani da wayarka ko kuma computer dinka don bunkasa kasuwancin ka musamman a wannan zamani da muke na internet a inda duk yawancin mutane sun yi connecting da internet kuma a kusan kullun harkokin kasuwanci bunkasa suke a internet wanda ke da  wata tambaya sai yayi a comment section na wannan website din.