Table of Contents
Man shafawa: Yadda ake fara kasunacin hada man shafawa a samu kudi dashi
sosai
Kullun kusan ana amfani da man shafawa wannan wannan ke nuna muhimmacin shi a rayuwar alumma musamman a lokacin sanyi domin kare fata daga bushewa wanada hakan ke haifar da kay kaya.
Dalilin haka ne masu hada man shafawa suna samun kudi sosai saboda yawan amfani da ake da shi da kuma rashin yawan masana’antun shi mussamman a Nigeria da makwabtanta irin su niger.
A dalilin haka ne mai karatu zamu yi maka bayanin kayan da ake hada man shafawa da kuma yadda zaka fara kasiuwancin ka domin samun riba da kuma kimar da yakamata ka fara in kai karamin dan kasuawa ne kafin ka kai ga babba.
Amma kafin muyi bayani akan yanayin kayan ko sinadaran bari infara lissafa maka su da kuma dan takaitaccen bayanin su
Kafin nan ana iya karanta yadda ake hada gurguru itama wata sana’a ce da muka koya wadda ana samun kudi da ita sosai da kuma yadda ake hada Air freshner in baka iya ba ka koya suma.
Kayan da ake hada man shafawa da su
1. Tuwon Mai (petroleum Jelly
Tuwon mai kusan ma shi ne za’a ce jigon man shafawa wanda kusan shi ke taka rawa kashi saba’in a cikin hadin. tuwon mai dai kala biyu ne wanda sune fari da kuma dorowwa, wanda ya danganta ga yadda shi wanda zai hada mai wane kala yake so fari ne koko dorowwa dukan su ana amfani dasu ne don hada man shafawa.
2. Ruwan mai
Sinadari na biyu shi ne ruwan mai wanda ake amfani da shi wajen hada mai inda a yanayinsa bashi da kala lamar yadda kaga ruwa hakayake amma shi mai ne, ana zuba shi ne a cikin kayan hain mai don ya kara ingancin tuwon mai.
Da dama ma idan kanaso man ko kuma shi tuwon mai din yatyi maka afki sosai kana iya zuba ruwan mai din da dan yawwa, sai ka kara wax wanda shi zai taimaka maka ka jalafta tuwon mai din, kwantar da hankalinka zamu yi bayani sosai a wajen yadda ake hadin sinadaran kayan man shafawa wanda mun yi post a kan shi a wannan website din ta hausawasite.com.ng kana iya danna link din ka shiga ka koya.
3. Wax (candle wax).
Wax(candle wax) dai wani sinadari ne dunkulalle wanda shima ana hada man shafawa da shi, a yanayi yana da tauri kuma yana da farin kala a zahiri. Ana kiran sa ne candle wax a dalilin ana amfani da shi har a wajen hada kendir to ana hada mai da shin shima.
4. Turare
urare na da matukar amfani wajen sa abu yazama mai kamshi ba ma mai kawai ba abubuwa da yawa da ake hada su don sama jiki ko kuma sama wuri ana yawan amfani da turare don kamshi rahama ne. To dangane da man shafawa ana sa turare ne gwalgwadon yadda ake so aji kamshin man.
kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu
yadda ake samun kayan man shafawa
Ga masu son fara kasuwanci na man shafawa yana da kyau su san sinadarai ko kayan da ake hada shi da kuma inda zasu samu su wanda wanda na lissafa su a sama lissafa jerin kayan ko kuma sinaran da akae hada man shafawa verselin da shi, yanzu kuma zamu yi magana akan yadda zaka fara naka a mtsayin karamin dan kasuwa dan kadan
Kimar yawan yadda zaka fara kasuwancin man shafawa ga karamin dan kasuwa.
To ga karamin dan kasuwa ina iya baka shawara kada ka fara da yawa sosai domin shi kasuwanci farko akwai bukatar a koye shi ko kuma a gane yadda yake tafiya.
To ni dai ina iya baka shawara ka fara da kilo ukku ko biyar haka wanda sune dai dai don yi da kuma fahimta ko kuma ma daya.
Hadin Kilo Dozen Nawa Yake Dauka na Robobi
To gaskiya akwai hadin da muke hadawa na kilo wanda ya kunshi duka kayan hadin da ake bukata domin hada man shafawa kuma duk kilo daya yana daukar roba dozen ukku na kananan robobi sai manya dozen biyu
Ina zaka samu sinadaran
Sinadaran hada man shafawa ana iya samun su a kasuwa idan kasuwar akwai masu saida chemicals din ya danganta domin ba kowace kasuwa ake samun su ba amma ga wanda bai san inda zai sawo su ba yana iya saye daga wannan website din a kowane gaeri kake a kaima kayanka domin akwai direbobi wadanda ake ba su kai kaya a garuruwa daban daban ga lambar waya ta kira da whattsapp dama Email a kasa zani bayar don tuntuba game da samun sinaran ko kuma masun neman karin bayani.
ADDRESHIN DA ZA’A SAMU SINARAN
Lambar waya
+2349037157675+2349072783217Websiteku biyomu facebook
Email address
Tura a shafukar sada Zumunta
↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin