Table of Contents
Sabulun wanki: Yadda ake hada sabulun wanki na saidawa
Kamar yadda aka sani a wannan website din ta hausawasite.com.ng muna koya sana’oi da dama a cikin harshen hausa domin taimakama alumma musamman matasan hausawa su samu aikin yi shiyasa muka sa ma website din hausawasite, misali kamar akwai inda muka koya Yadda Ake fara kasuwancin saida man shafawa Verseline to a wannan post din ma inshallahu munzo da yadda ake sabulun yankasuwa wanda suke saidawa zuwa ga kostomominsu, wanda wannan zai dan banbanta kadan ga wancen post din da mukai na yadda ake hada sabulun wanki.
Kuma har ila yau zamuyi bayani gamsashe akan inda zaka samu sinadaran da zaka hada sabulun ka cikin hanya mai sauki
Tsokaci kadsana game da sabulun wanki
Kamar yadda kowa dai ya sani ana amfani ne da shi wajen yin wanki, kuma shi na amfanin kullum ne lokacin sanyi ne koko a lokacin zafi duk ana amfani da sabulu don a wanke kaya domin ba mai bukatar kazanta,
kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu
kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu
Sinadaran da ake hadawa da su
Da farko yana da kyau mai son ya hada ya sani sinadaran da ake hadawa subada sabulu, shiyasa zamu fara jera su sannan mu tafi akan yadda ake hada kayan su koma sabulun wanki lafiya lau.
Ga sunan lissafe a kasa.
Lissafin sinadaran da ake bukata.
1. Costic soda
2. Soda ash
3. Sulphat
4. Silkate
5. Man kwakwa
6. Kala (ta ruwa gamasu bukata)
7. Kwankwani
8. Roba ko mazubi
9. Ma’auni(misali lidde)
10. Safar hannu
Matakan da ake bi wajenh Tsimin sinadaran su koma sabulun wanki
Tunda munga jerin sinaran da ake bukata wajen hada sabulu yazu kuma inshallahu zamu yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsuma sinadaran.
Dafarko dai zaka samu erobobin ka guda ukku lafiyayyu ba dole sai ruba ba mazubin ka guda ukku, bayan ka samesu sai ka samo ruwa shima ka aje a kusa da kuma abunda za ka yi amfani da shi a matsayibn ma’auni kar ka canzashi har mu gama misali lidde ko wani kofi idan ka tanaji wadannan abubuwan da na ambata to sai mu je a cikin aiki;
A Kula a nan zan yi amfani da lidde a matsayin ma’auni na
To ga matakan da yakamata mai karatu ka kiyaye kuma ka bi su sau da kafawajen hada sabulun ka,
1. Mataki na daya
Zuba lidde ko ma’auninka ukku na ruwa a cikin roba ko mazubi na daban, sai ka deba costic soda liddeukku itama lidde ukku ka zuba a cikin ruwan da ka zuba a robar.
2. Mataki na Biyu
Dauko debo ruwa kashi daya bisa hudu(1/4) na ma’aunin da kai amfani da shi na costic soda ka zuba a cikin wata robar har ila yau itama soda ashe kadebo kashi daya bisa hudu ka zuba a cikin ruwan, itama sulphat kayi mata irin na soda ash.
Bayan kayi haka sai ka zuba su a wurin da ka hada costic soda din ka.
3. Mataki na ukku
Ka dauko silket shima kashi daya bisa hudu(1/4) na ma’auninka ka sa a cikin ihadin gukan su.
Daga nan kuma sai ka dauko man kwkwar ka ka sa ma’auni biyu a cikin kwabin da ka yi, ka zuba kala taruwa in kanason yayi kala da kuma turare ga me son kamshi, to sa ka cigaba da motsawa zakaga ruwan yana warewa daban sablun yana dunkulewa.
Da kaga ya dunkule wato sinadaran sun hade sosai sai ka samu kwankwaninka ka rinka zuba hadin ka ajiye shi har sai ya bushe to inshallahu zaka ga sabulunka ya hadu lafiya lau in kasa kala zaka ga yana da kala in kuma ba kala zakia ganshi fari yayi tauri sai ka saida.
Domin fahimtar inda ake saida sinaran duba bayani akan Yadda ake samun sinadarai ko kuma kayan hada man shafawa
kuna iya kasancewa da mu a shafukan sada Zumunta a
Domin fahimtar inda ake saida sinaran duba bayani akan Yadda ake samun sinadarai ko kuma kayan hada man shafawa
kuna iya kasancewa da mu a shafukan sada Zumunta a
Lambar waya
+2349037157675+2349072783217
WebsiteEmail address
Tura a shafukar sada Zumunta
↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin