Skip to content
Home ┬╗ Yadda ake samun Sinadaran da kuma kayan hadin sabulu ko man shafawa a cikin sauki

Yadda ake samun Sinadaran da kuma kayan hadin sabulu ko man shafawa a cikin sauki

   Assalamu alaikum Jama’a a wannan post din zamu kawo maku hanyoyin da zaku bi don sa,mun sinadarai da kuma abubuwan da kuke bukata na asana,oin ku  musamman sana’ar hannu ta gida, irinsu kayan hadin man shafawa sabulun wanki da ma sauransu.

kayan hada man shafawa ko kuma sabulu

Dalilin hakan shine mutane da dama suna tambaya akan ina zasu samu kayan da zasu fara sana’ar su to shiyasa muka ga akwai bukatar ayi bayani gamsasshe akan hakan saboda a wasu wuraren suna matukar wahala a same su a cikin sauki.

kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai  Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu

Wuraren da Ake samun Sinadaran ko kayan

      Ya danganta akan inda mutum yake so ko kuma abunda mutum yake son ya saya da kuma abunda yake son ya hada ga jerin wuraren kuma da dan takaitaccen bayaninsu kamar haka.
  • kamfanunka.
  • Online.
  • Kasuwa.

  • Kasuwa
Zaka iya samun wurare ko kuma shaguna daban daban inda zaka sayi sinadaran mussamman swhagunan da ake saida chemicals ya danganta ba a kowace kasuwa ake samun su ba amma dai a babbar kasuwa ta garuruwa da dama ana samun masu saida chemicals ko sinadarai.
Sai dai kafin ka sawo yana da kyau ka san yanayin, awo ko kuma kimar da zaka zaka sawo su domin ba kowane ,mai saida chemicals ne yake iya hada abubuwan da yake saidawa ba.

  • Online 

kamar yadda kowa ya sani yanxu cigaba ya zo na yanar gizo inda zaka iya sayen abubuwa da yawa a online har gida a kawo maka.
A fdalilin haka ne a wannan website din ta Hausawa Site muka kawo wani sabon shiri wanda zai taimaka ma daliban mu hanyar samun sinadarai ko chemicals a cikin saukin kusan a kowane gari kake a fadin nigeria cikin ikon Allah. Ga yadda abun yake kamarv haka:-

  1. Bayan ka karanta post a sana’ar da kake son farawa.
  2. Sai ka Tuntube mu a lambar waya ko kuma ta kafar sada zumunta ko email ga su kamar haka
Lambar waya: +2349037157675
  1. Bayan Tattaunawa da fahinta tsakaninmu da kai wanda ya hada da yawan sinadaran da kake so da sauransu.
  2. Sai kuma ka fadi addreshin da zamu sa Direba ya kaimaka

  • Kamfanunnuka
wuri na ukku kuma shine ta hanyar tuntubar kanmfanunnukan da suke hada sinadaran wanda gaskiya ya dan fi wahala akan wadanda muka ambata a baya saboda shi dole sai kana da addreshi na kamfani wanda yahada da lambar waya da sauransu kuma yawanci hakan na yuwuwa ne idan kahadu da kayan da suka hada a hannun wani ko kuma ta hayar binciko su a Google ko kuma ashafukan  su na sada zumunta irinsu facebook.

Kammalawa

To anan muka zo karshen wannan post din wanda mukai bayani akan 

Yadda ake samun Sinadaran da kuma kayan hadin sabulu ko man shafawa a  cikin sauki kuma duk wanda yake da wata tambaya ko kuma karin bayani yana iya rubutawa a comment section na kasa kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa da mu a wannan website ta hausawasite.com.ng.