Table of Contents
Man Gashi: Yadda Zaka Fara Kasuwancin Hada Man Gashi ko man
kitso
Assalamu Alaikum Jama’a a yau ma muna tare da wani sabon kasuwancin inda zamu koya yadda ake hada man gashi ko kuma man kitso na saidawa in dai ba’a manta ba a baya mun koya yadda ake fara kasuwancin man shafawa inda mukai bayani gamsashe a kan sana’ar.
Dafarko Bari mu fara lissafa sinadaran sannan mu tafi akan yadda ake hadin su.
Kayan hada man Gashi ko man kitso
Bari mu lissafa kkamar misalin na kilo daya 1.
1. Tuwon mai (1kg)
2. Ruwan Mai =(75cl)
3. Wax
4. Glaserene ko Vitamine E.
5. Bakar Kala ta mai
6. Menthol.
7. Comphor
8. Sulphur
9. Turare.
Yadda ake Hadin Sinadaran
Da farko dai a fara sa ruwan mai da wax a cikin tukunya su fara narkewa sai a kawo tuwon mai a zuba a ciki shima, da sun narke duka sai a dan sauke Tukunyar kasa.
A dauko menthol a zuba a cikin turare tare da comphor a karkada sai a zuba a ciki’
Sai a dauko Glaceren ko Vitamin E wanda a ka baka ya danganta a zuba a ciki.
Sai kuma daga nan a jika sulphur a zuba a cikin hadin itama
Da karshe kuma sai a dauko kala a zuba a cikin hadin duka a cigaba da motsesu sosai daga nan kuma sai a samo robobi a zuba a cigaba da saidawa.
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin