Skip to content
Home » Yadda zaka habaka kanka ta fuskar karatu da bincike a koda yaushe ta hanyar amfani a yanar gizo

Yadda zaka habaka kanka ta fuskar karatu da bincike a koda yaushe ta hanyar amfani a yanar gizo

 

Yadda zaka habaka kanka ta fuskar karatu da bincike a koda yaushe

Assalamu Alaikum jama’a masu ziyartar wannan shafi mai albarka barka da wannan lokaci barka da zuwa hausawasite.com.ng mujalla kuma shafi na yanar gizo da ke kawo maku muhimman abubuwan karuwa, yau inshallahu zamu yi magana dangane da muhimmancin bincike ta yadda zaka habaka iliminka a koda yaushe.
Akwai post ma akan yadda zaka hab
baka kasuwancinka ta hanyar bude facebook page
Tabbas karatu yana da matukar amfani kuma ilimi shike kan gaba kuma ko shakka babu hada mai ilimi da wanda bashi da ilimi ba abu ne mai yiwuwa ba, don wanda ya sani yafi wanada bai sani ba ta kowace irin fuska.
A da mutane suna matukar shan wahala kwarai kafin su samu ilimi wanada shine mabudin habbaka 
rayuwa, amma yanxu kusan abun ya canza zane inda a wayar tafin hannunka ma sai kayi karatu wanda zai taimaki rayuwarka harma da sana’arka.
Domin a yanzu kana iya amfani da wayarka ka koyi ko abubuwan da kake bukata a yanar gizo kama daga sana’oi da sauransu, 
Misali a wannan shafin na yanar gizo ko ita kanta muna koya sana’oi musamman don matasa ta fusakar da zasu inganta rayuwar su  kamar yadda ake hada man shafawa, yadda ake hada air freshener da sauransu.
To bari muyi duba akan abubuwan guda ukku Wanda sune muhimman da zasu taimaka Maka wajen binciken kominene.
Karanta

Abubuwa ukku masu mahimmanci

1. Google( search engine )

A yanzu kusan duk bayanini da kake bukata mafi akasari kafi saurin samun shi a yanar gizo inda shafuka na nema (Eearch Engine) irinsu Google suke taka rawa kwarai da gaske domin su suna nemo bayanan shafuka na website wadda suka bada damar a yi amfani da su in mai nema yazo batare da biyan ko sisi ba.

Amma fa yana da kyau wajen abin da kake bincike a kanshi kayi taka tsan-tsan don akwai bayanai bana daidai ba.

2. Bidiyoyi

A fanin video suna taimakawa sosai don musamman yanzu kowa yafi son ya kalli  video a want lokacin idan abu ne irin na aikace irinsu YouTube sunyi zarra wazen kawo bidiyoyi da dama.

3. Littattafan PDF

Littattafan PDF suna taka rawa sosai Kuma mafi yawanci ko Ni kaina na karu dasu Kuma a duk lokacin da ka dage ka karanta littafi daga bango zuwa bango ma’ana duka to zakaga ka karu sosai.

Suma kawi safukan yanar gizo Wanda zaka iya sauke littafi na karatu musamman na computer sauransu kyauta kamar computer-pdf.com suna bada damar hakan Suma.

4. Shafukan Tambaya da Tattauna Batutuwa(Online Forums)

Tabbas wadan shafuka(website) na tattauna batutuwa suna da amfani domin duka abunda ya shige maka daka tambaya za’a baka amsa ba da dadewa.
kuma zaka iya amfana da tambayar da wani yayi ire-irensu sune Quora.com, Starkoverflow.com da ma sauransu.