Table of Contents
Fahimtar yadda shafukan yanar gizo suke aiki kafin ka koyi bude su
Assalamu alaikum kamar yadda aka saba yau ma ni Ibrahim Buhari mu tare a cikin wannan posting din wanda inshallahu zai kara fayyace bayani akan yadda website ko blog yake wato a hausance shafukan yanaar gizo domin kafin ka bude su yana da kyau ace ka san hakan.
Idan ba’a manta ba a baya mun koya yadda ake bude shafin website blog wato na kyauta a blogger ga yan koyo.
Kuma inshallahu littafin Pdf na nan tafe acigaba na kan website dama sauransu a cigaba da kasancewa damu a www.hausawasite.com.ng a koda yaushe don samun abubuwa masu amfani.
yana da kyau mai karatu ya natsu ka karanta duka in kana son ka gane.
Mi ake Nufi da Shafin yanar gizo Website/Blog?
- Website
- Blog
wadannan kalmomi suna da alaka kusan ma kamar duk daya ne amma kanatsu zaka gane banbancinsu.
Minene Website?
Minene Blog?a
Blog to shima kamar website ce a server aka dora kuma an hada shi da domain kamar .com.ng misali hausawasite.com.ng wadda ita mafi yawanci inda ya bambamta da website kawai shine rubutu ake yi bayan lokaci lokaci labarai ko abubuwan amfani.
Amma shima ana cemasa website shine babban sunan
Karanata:
Yadda shafin yanar gizo Website ke Aiki
Shafin yanar gizo an hada sune da programming language wanda ake cema HTML shine yaren da akayi amfani aka gina su.
To inda ake aje wadannan filoli a wasu manyan computers ne wato na’ura mai kwakwalwa babba wadda ake cema server.
Ita kuma server kullun a duniyar nan kunne take saboda kar a nemi bayani a rasa a kunna su wanda in akace internet yanar gizo duka ana nufin computocin duniya da suka hadu suna musayar bayanai.
To kaji dai shi shafin an dora shi a computer to bari mu tafi akan yaya kake samun abun in ka rubuta a manemarka Browser kenanan kamar opera tunda a ciki zaka nemi shafin da kake son ziyara ko
Abunda ke faruwa in ka rubuta addreshin website ?
To su zasu nemo maka server wadda take aje da files na www.hausawasite.com.ng wadda ka rubuta sai ita kuma ta taji ana neman shafin.
Sai ta maido maka da wanda ka nema taba ISP daga nan ya shigo browser wadda ita zata fassara maka file din programming din dana ambata a baya.
Sai kaga Hoto, rubuto, video da sauran abunda shafin ya kunsa kamara yadda kaga hoton kasa yanuna shafin farko na wannan website.
wannan a na gaba a cigaba da ziyartar website din inshallahu zamuyi maganarsa.
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin