Skip to content
Home » Yadda ake amfani da Google Drive don aje waka hoto video ko filolo ajiya ta har abada

Yadda ake amfani da Google Drive don aje waka hoto video ko filolo ajiya ta har abada

    Google drive Ana amfani da shi ta fuskoki da dama Wanda yawancin amfanin shi shine a aje ko a adana file ko Kuma hoto har ma wakoki da karatu , kai har ma video domin amfanin gaba idan ana so ayi amfani da abunda aka aje a gaba.

A dalilin haka a wannan post na wannan website din wato Hausawasite.com.ng muka yi shi akan yadda zaka iya amfani da google drive dinka don aje abubuwan amfaninka wanda duk lokacin da kake bukata indai ka dora su to inshallahu zaka samesu a cikin sauki in  ba’a manta ba a post din mu na baya munyi magana akan yadda zaka habbaka kanka ta fuskar bincike 

Yadda ake aje hotuna ko na buduwa ko mace a google drive

Tsokaci Kadan Gameda Google Drive 

Google Drive dai daya ne daga cikin kayan Google ko kuma ince apps na Google wanda kamar yadda na ambata a baya ana aje kowane irin nau’in file a saman shi domin kudun rasa wannan file ko kuma don turawa mutane dayawa su ga file din har mu sauke shi a cikin watar su ko kuma computer dinsu domin suma suyi amfani da shi.

Kafin ka samu damar amfani dashi dole sai kana da gmail account wato na google kenan samun shine zai baka damar amfana da google.

Kyauta ne ake amfani da shi suna baka 15GB kyauta in kuma kana son ka wice haka kana iya biyansu sai su kara ma damar ajiya to tunda mun ga matashiya game da shi bari mu tafu akan yadda zaka safke shi da kuma yadda zaka yi amfani da Google drive din.

Matakan da zaka bi don Dora Abubuwan amfaninka

  Matakan da ake bi ga su nan a kasa zamu lissafa daki daki tare da nuna hotunan dan sawakewa.

Da farko dai zaka je Playstore kayi install din app din kamar yadda hoton sama ya nuna zaka rubuta Google Drive a search inda ake bincike bayan ka Yi install ka safke shi kenan  a cikin wayar ka sai ka shiga a ciki kayi login
Bayan ka sauke shi a cikin wayar ka idan ka bude zaka ga kamar haka ansa alamun plus sai ka danna nan  zai bude maka wasu options abubuwan da zaka iya kara yi kuma.

Daga nan kuma bayan ya bude maka haka zakaga options da zaka iya zaba akwai folder idan folder duka zaka dora sai ka dannna ko kuma akwai upload idan zakayi uploadin din video ko kuma waka ko ma ince duk wata audio.

Sai kuma akwai irinsu Google Docs abubuwan dakayi typing, sheets kamar su excel format sai kuma irin su slids. Amma dai kana iya amfani da Upload kawai in kana so ka dora.

Da kayi wannan kuma sai matakin karshe inda zai kawoka a inda zaka zabi file dinda kake son ka daura sai ka zaba ka daura shi kamar yadda kibiyar hon kasa ta nuna

Karanata

Kammalawa

Kammar yadda bayani ya gabata a baya munyi bayani akan yadda zaka yi amfani da Google drive don ajiya koa adana abubhuwanka wanda suna baka kyautar storage har kusan 15GB don adana abubuwanka kuma kana iya tura link din abun zuwa sauran mutane suyi download ta hanya mai sauki wanda yake da tambaya sai yayi a comment section.