Table of Contents
Yadda Zaka Hada Facebook Page Don Habbaka Kasuwancinka
Assalamu Alaikum jama’a kamar yadda kowa ya sani facebook page yana da matukar amfani musamman ga mai kasuwanci,
Domin yana taimakawa wajen samun customers masu yawa wanda zasu sayi hajarkadalilin ana iya ganin abunda ka dora a fadin duniya bakidaya.
Domin ta hanyar mutane ne kadai zaka iya saukin samun sayen abunda kake saidawa a yanar gizo bama a yanar gizo kadai ba kai har ma a kasuwanci na kasa wato ofline, bari in baka misalan amfani kafar sadarwa a matsayin wajen tallar fiye da ta kasa irinsu radio misali.
Amfanin Cin Moriyar Kafar Sadarwa ta Yanar Gizo(online) fiye da ta Kasa(ofline) Musamman Facebook Page.
- Babu madakata akan iya abunda zaka iya samu a shafinka na facebook ko twitter saboda yawan mutane.
- Idan ka dora haja za’a iya ganinta a koda yaushe ba rana ba dare.
- Zaka iya amfani da tallar da kamfanin facebook yake ga yan kasuwa don kayi target na customominka garin da kake so shekarunsu da sauran abunda zai taimaka maka duka zaka iya sawa kawai zaka biya su kudi yadabganta ka yadda ka tsara.
- Irin wadannan kamfaninnuka suna maka talla ne ga masu son abun saboda sun sana abunda kowa yake so.
- Suna da saukin talla da kudi kalilan ba kamar kaje gidan radio ba su da kasa da dubu kana iya farawa ma.
To tunda munga mahimmacin amfanin da facebook page din bari mu tafi akan yadda zaka bude shi.
Yadda Zaka Bude Facebook Page
Da farko dai ka tabbatar ka bude Facebook kayi register kana da accont sai kaje kayi login ka shiga a ciki wato kayi login.
Bayan kayi login sai ka danna sashen Menu zakaga options
Daga nan kuma sai ka zabi Pages
Sai kuma ka zabi Create wanda nan zai kaika inda zaka fara cike- cike
Bayan nan kafin ka fara cike-cike zai nuna maka rubuce rubuce na gabatarwa sai ka danna skip sau kamr ukku in kla gansu.
Daga nan sai ka sunan da kakeson ka sama shafin facebook dinka ab=nso ka samashi sunan kasuwancinka.
Daga nan sai ka zabi a wane fanin kasuwanci zakayi amfani(categories) Abubuwan da zai kunsa kenan.
Daga nan in kana da Shafin yanar gizo(website) itama sai ka rubuta Addreshin ta Inda aka sa Enter Address
Daga nan sai ka danna ka zabi hoto ka sa ko kuma in baka shirya sawaba kana iya wucewa ko gaba ka sa wannan.
Da ka yi wadannan matakan to ka kammala bude shafin facebook dibnka sai ka fara rubuta posts kana gayyato abokai kuma kana watsawa.
Karanta
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin