Sayen Computer yana da amfani sosai musamman ma ga dan kasuwa wanda yake wata sana’a wadda ta kunshi amfani da computer kamar kasuwancin printing da photocopy.
Amma kafin ka sayi computer shin second ce ko sabuwa yana I da kyau ka tsaya ka lura da wasu abubuwa game da ita, kuma ka fahimi ya suke aiki musamman ma idan dama kafin sayen kana da sanin computer ko yaya ne.
Wadannan muhimman abubuwan da zaka duba suna zasu nuna maka shin mai lafiya ce, zatayi kwari koko tana da wani rauni.
A dalilin haka ne a wannan post zamu yi dubi akansu yadda inka tashi saye zaka iya gane computer mai inganci da kuma lafiya, kuma kawai bayani akan yadda zaka habbaka kanka ta fuskar bincike.
Kuma muna baka shawara ka tsaya ka natsu ka karanta bayanin daga farko har karshe don fahimtar shi da kyau.
Table of Contents
Muhimman Abubuwan da ya kamata ka duba a lissafe
Abubuwan da zakayi la’akari da su gasu kamar haka zamu fara lissafawa kafin bayani.
- Wane kalar girma gareta
- Yawan processor dinta
- yawan kwakwalwar ajiyar ta Hard Disk
- Yawan RAM wato ma’ajin aikinta
- Batir dinta da yanayin rikon caji.
Bayani game da su
Ga bayanansu nan zani yi daya bayan dauya yadda zaka fahimci abun sosai domin kafin ka sayi ko wace irin computer gaskiya yana da kyau a ce ka fahimci wadannan abubuwan da zan yi bayani akan su saboda ita fa ba kamar wayar hannu ba ce.
Karanta: Abubuwa 5 da suke sa dan koyon computer ya kware
Karfin Processor
Processor wani abune kamar kwakwalwar na’ura mai kwakwalwa computer wanda shike kula da aikace-aikacen da take yi raunin shi sosai matsala ne.
![]() |
Hoton Bayanan Computer ciki hadda yawan processor |
Don haka yana da kyau ka lura da karfi ko yawan processor na computer kafin ka saye takuma ka lura wane irin kamafani yayi shi, bari in danyi tsokaci game da kamfanunnukan da suke yinsa sanannu.
Sanannu kamfani sun hada da Intel da AMD.
Amma computer wadda akayi da processor na kamfanin Intel tafi Inganci da saurin aiki fiye da kamfani AMD.
Bayan ka zabi kamfani to sai maganar yawan processor din to a gaskiya ya danganta da abunda zakayi akalla idan manyan softwayoyi zaka sa ka samu biyu amma kar ka damu 1.5 ma lafiya lau amma dai domin karfin computer biyu zuwa abun da yayi sama.
Yadda zaka gane yawan a windows dai-dai this pc ko my Computer zaka danna properties zaka gani.
Karanta: Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su
Yawan Hard Disk
Yana da kyau ka sani c ewa hard disk shine ma’ajin karshe wato inda ake aje abubuwan da kayi saving wanda suka hada da hotuna, filoli ko bidiyoyi duka a nan ake aje su.
Kaga yana da kyau wajen sayen computer ka sayi mai yawa musamman in zaka aje abubuwa da yawa dudda dai shi kana iya kara sayen wani ka saya kamar memory yake kana iya cirewa ka canza koda yaushe.
Shikuma karami shine kasa da dari to akalla ka tafi dari anuda yayi sama ina baka shawara ma da zaka samu kamar dari biyu da yafi.
Yawan RAM
RAM wani ma’aji ne a lokacin da kake aiki da computer shi zai rike aikace akacen da kakeyi daka danna save sai ya maida ajiya zuwa Hard Diska wanda mukayi bayani a sama.
Kaga yana da amfani sosai shima kenan shima kuma ana iya karawa musamman ga laptop amma ka kula wasu komputocin suna matse ram dinsu misali suke 3GB ne karshe.
To idana zaka sayi computer ka duba properties kaga yawan RAM dinta gaskiya 2GB yafi dadin aiki idana yayi kasa da haka bawai kai tsaye zance da matsala ba amma baka jin dadin aikinta ta fuskar sauri misali kamar Browsing da downloading.
Batir dinta da yanayi rikon caji
Kammalawa
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin