Skip to content
Home » Artificial Inteligence: Bayani game da sama computer tunani kamar na mutum

Artificial Inteligence: Bayani game da sama computer tunani kamar na mutum

 A shirin labaran mamaki na wannan nako munyi dubi akan fasahar da ake sama na’ura mai kwakwalwa wato computer su zama suna aiki ko tunani kamar na dan Adam kamar yadda in ba’a manta ba baya munyi magan akan jirgin da ya bace ya dawo dawo bayan shekara 37 lafiya lau da fasinja ba wanda yayi wani abu kana iya duba shi.

Inda irin wannan fasaha ana amfani ne da ita mafi akasari inda mutum baya iya saurin yin abu kokuma sai ya wahala yake samun damar yinsa.

A wannan fasaha zakaga misali kamar sakago wato robot a samashi ya koyi yare kuma ya rinka yin yaren da mutum lafiya lau.

Bama haka ba a yanzu ma kusan a cikin wayarka akwai abubuwan ko ince manhajoji wasu duk ana samasu irin wannan fasaha musamman manhajojin kamfanin Google.

Bari  mu dauki Google assisstance a matsayin misali.

Misalin Manhajar da ke amfani da Artificial Inteligence

Google Assistance

Google assistance a wasu wayoyin android din wadanda suka kai version 8 haka zaka ga akwai shi in ma babu shi kana iya downloada a nan.

Wannan manhaja mallakar kamfanin Google ne domin kara bunkasa binciken da mutane keyi a yanar gizo.

Shi ana amfani da shi ne wajen kamar kana neman bayani a internet daka yimasa magana da turanci zai nemo maka abunda kake so babu bata lokaci.

To kaga irin wannan dayaji magana ya baka amsa ta hanyar bincike kuma ya gaya maka amsar ta magana an amfani da fasahar Artificial inteligence wato computer tayi aiki kamar na mutum.

Karanta: Yadda dan shekara shidda ya tuka jirgi