Skip to content
Home ┬╗ Yadda ake Installing Software a cikin computer da Abubuwan da ya kamta ka sani

Yadda ake Installing Software a cikin computer da Abubuwan da ya kamta ka sani

     Downloading da installing din software abu ne mai amfani ga kowane mai amfani da computer domin kara wasu manhajojin software wanda zasu taimaka mashi wajen aikin yau da kullun, byan ka samu computer mai kyau yana da mahimmaci ka samata software masu inganci tsaftatattu daga virus.

Domin yana da mahimmaci mai karatu ya san cewa itama computer virus yana kamata kuma yana hadasa mata masaloli da dama kamar dadewa kafin budewa, yawan tsayawa a lokacin amfani da ita dama sauransu duk suna daga cikin illar virus a na’ura mai kwakwalwa.

Downloading Software

To shiyasa kafin ka sauke software ko kayi installing yana da kyau ka lura da abubuwa kamar gaka bayan mun ambata su sai mu tafi a wajen safkewa da installling.

Abubuwan Lura kafin sauke software

Yana da kyau kafin ka safke wata softaware a cikin computer dinka ka lura da wadannan muhimman abubuwan da zan lissafa su a kasa:
  • Wane kalar Operating System gareka
  • Ina zaka samu software din ko kuma ka samo ta
  • Nauyinta kamar nawa ne
  • Shin ta kyauta ce ko kuma ta kudi

Bayani game da su daya bayan- daya

Kamar yadda muka ambata su abaya to ga takaitaccen bayani gameda su.

Wane Irin Operating Sysyem gareka

Kafin ka safke wata software ya wajaba dolene kasan wane opearating system kake amfani dashi wanda zaka safke ita manhajar software din a ciki.

Domin idan ka dauko ta wani kasama wani baza ta yi ba, misali ka dauko software ta Windows ka sama Linux  baza tayi ba kwata-kwata dole sai ta windows din kuma ta irin processor din misali akwai x64 da x32 bit domin ka gane samfarin operating system da abubuwan da suka shafi computer dinka a windows kawai zabi computer ko this pc sai ka danna options sai ka zabi properties zaka gani.

Ina zaka samu software din ko kuma ka samo ta

Yana da kyau kasan cewa kafin a safke software ana taka tsantsan da don tsoran cutarwar virus na wai ko daga ina ta taho na kawai ka samo ka daura ma na;urarka, kuma yana da kyau ace kayi installing na wata manhaja wadda take yakar Virus wato Anti-Virus Software.
Sa wannan yana taimakwa wajen ko ka samo mai illa ta nuna ma ka cireta, to a fannin inda zaka samu ita sopftaware din kuma ya danganta yawanci kwara kaje shafin ita manhajar software din kayi Downloading.
In kuma ba haka ba to kana iya samun wanda ka yadda dashi ya tura maka wanda kuma shima lafiya lau computer dinshi take.

Nauyinta kamar Nawa ne

Yanna da kyau sosai kasan nauyin software kafin ka safke ta kuma kaima kana da wuri a cikin computer dinka.

Bama a nan abun ya tsaya ba kai har ma RAM dinka ya kamata ka san ita nawa ne kamar take bukata ga manyan softwares kai kuma nawa gareka.

Domin in manya ne wasu ko kayi Downloading sai suyi ta tsayawa ko ma su jamaka matsala wadda zata iya lalata maka computer dinka gaba daya.

Shin ta kyauta ce ko kuma ta Kudi

Wannan ma wani abun dubawa ne Daomin idan wasu softwayoyin wadanda suka yi su kyauta suke watsa su ba tare da an biya ko sisi ba.

To wasu fa na kudi ne kuma gaskiya yawsancin softwayoyi na kudi ne ba na kyauta bane wato shine ake cema licebse in ka ji kana iya saye kana iya saye ta shafin yanar gizon manhajar shikenan.

Yadda zaka yi Download da Install

A nan zamu koya wanda zakayi download a cikin sauki wanda website din in kaje suna gane da wane operating system kake amfani, misali kamar a nan mun dauki chrome Browser ga kuma matakan da zaka bi.
Shiga Browser Software a cikin comfuter ka sai ka danna Download sunan software din misali ni anan nasa Download Chrome Browser.

Bayan ka rubuta ka danna enter to zakaga ya kaika shafin zaba a Doogle din to a nan mafi yawanci website ta sama ita ce ta sofware din inda ake samun ta.
To sai ka danna ka sihiga.

Daga nan kuma daka danna zakaga ta fara sai sai kabari ka ida.
Da zaran ta Ida sai ka shigaDownloads folder a cikin computer dinka sai ka danna ok in kuma oermissin tace sai ka sa allow, daka yi haka sai kayi accept license sai kuma next har ka gama shike nan sai ka bude ta.