Skip to content
Home » Yadda ake Connecting din Computer da Internet

Yadda ake Connecting din Computer da Internet

Yadda ake connect din computer

 

A zamanin yanzu internet tana taka rawa sosai Wanda mafi yawancin abubuwa ana amfani da internet ayi sukama daga fannin ilimi, sada zumunta dama sauransu.

Kamar yadda a baya muka koya yadda are hada ko kayi connecting na Wi-Fi da Hotspot a waya to a yau game da masu computer inshallah zamuyi bayani.

Wadanne Hanyoyi ne ake bi wajen sada computer da Internet?

Tabbas ba wai hanya daya bace kawai ake bi ba wajen hada computer da Internet akwai hanyoyi kwarara wadanda suke sannanu guda ukku wanda gasu kamar haka.

Ta Hanyar Wifi da Hot-Spot

Idan kana son kayi connecting computer da network ta internet kana iya amfani da wayarka idan kana da babbar waya haka kamar ta Android suna da WIFI da Hotspot zaka bude hotspot din wayaarka ne sai ka jona ta da computer dinka..

Akawi kuma wani abunda ake cema Router Idan kana da ita kana iya kunna ta ka hada ta computer dinka daya ko dayawa duk tana iya dauka a lokaci daya

Ta hanyar Bluethooth tarthering

Akwai watahanya wadda mafi yawancin android a yanzu suna da ita irace har ta bluetooth kana iya amfani ka kama yanar gizo lafiya lau kamar dai yadda kake amfani da wifi- da kuma hotspot.

Ta Hanyaw Cable na Hotspot

Hotsport guda biyu ne na saman da muka ambata wanda zaka kunna hotspot ne sai ka jona da wifi ta computer dinka amma akwai na cable idan ka duba a cikin wayarka sai jona da shi sh ka kunna data daga cikin wayarka.
Hada Computer da yanar gizo

Ta Hanyar Amfani da Moderm

Moderm dai wani abu ne wanda ga hotonshi Kamar haka shi ana samashi layi ne na MTN, Airtel , glo da sauransu ko wane layi dai Sai ka sa layin a ciki.
Moderm
Moderm yana da mayukar amfani saboda wani lokacin yafi ma waya saurin yin Browsing a cikin computer saboda si don haka ne aka hada shi. Tunda munga kala-kalar nauikan da ake connecting na computer da internet bari mu tafi zuwa matakan da ake bi domin hada computer da internet din ta hanyar modedrn.

Matakan da Ake Bi Don hada Computer da Moderm

Ga matakan da zaka bi nan domin yin connecting din computer ka da yanar gizo musamman masu amfani da windows operating system.

Mataki na Daya

To da farko dai bayan ka samu computer ya danganta laptop ce Koko desktop duka ana amfani da su.
Zaka samu moderm din ka sa wajen USB din computer din sai ka tsaya ka kula idan yayi connecting zai kaga symbol na kasarn task bar ya nuna abun service.
Da kasa layin to a nan ya danganta wane operating system kake amfani da shi idan Windows ne zaya maka installing directly idan Kuma Linux ne Sai ka je Edit connection sannan ka saita.

To misali a nan tunda yawancin da windows aka fi amfani na kamfanin Microsoft bari muyi amfani dashi.Sai ka danna connect bayan yayi install din software ta moderm din domin yayi connect a internet din.

Mataki na Biyu

Daga nan Sai ka shiga Browser ka cigaban da browsing, kana iya serch din url ko kuma ka shiga ta google kayi binken abunda kake son ka gano kana iya diuba koyon internet da muka yi a baya domin kara fahimtar abubuwan internet.

Abun lura

Kuma ya kamata ka sani bayan moderm dinka ya saitu zakaga connect da disconnect a setup softwarae da ya kamaka kana iya connect kana iya dissconnect