Skip to content
Home » Gyaran Gashi: Yadda ake wanke gashi da lalle ga mata

Gyaran Gashi: Yadda ake wanke gashi da lalle ga mata

Kamar dai yadda a baya a cikin wannan website mai albarka ta Hausawasite.com.ng muka kawo maku wasu daga cikin muhimman amfanin lalle ga mata to a cikin wannan post din na yau inshallahu zamu yi magana akan yadda ake amfani da shi wajen gyara gashi yadda zai maida gashin mai gyalli da kuma sulbi gwanin ban sha’awa.

Domin kamar yadda nike yawan ambatawa mata dole sai da iya Girki da kwalliya a duk inda suke saboda burge mai gida musamman ga matan aure.

Gashi

 

 

 

Kayan da ake bukata wajen hadin

Da farko inshallahu zamu fara da lissafa kayan da yakamata ki tanada kafin ki wanke gashin kuma gasu kamar haka:-
  1. Lalle kamar leda daya
  2. Rariya
  3. Ruwa kofi 1 da rabi

Yadda ake hada kayan

Ga matakan da zaki bi domin gyara gashi a lissafe tare da bayaninsu dalla-dalla yadda mai karatu zaya fahimta

Gyaran gashi

 

Mataki na Farko 1

Da farko dai zaki kwance gashin kanki ki sai ki samu masharci ki sharceshi ya shartu sosai ko kuma kina iya ba wata ta sharce maki.

Mataki na Biyu 2

Bayan kin gama yadda aka ambata a mataki na farko to sai ki samu lallen ki kamar adadin dana ambata a sama sai ki samu tukunya mai tsafta ki samu ruwa shima yadda muka ambata kofi daya da rabi sai ki daura a saman tukunya ki tafasa shi.
Karanta:

Mataki na Ukku 3

Da ya tafasa sai ki sauke shi ki zuba a cikin wani wuri ki bar shi yadan huce kar kuma ki bashi ya huce duka a da dan zafi kadan yadda baya cizon yatsa ake so, sannan sai ki dauko rariya ki tace shi.

Mataki na Hudu 4

Bayan kin tace shi sai ki dauko shi kina diba kina yabawa a saman kai sannan ki bar shi saman kanki har tsawon minti biyu haka.
Bayan yayi minti biyu haka sai ki samu ruwa ki wanke shi to a nan bayan kina gama wankewa idan kina da wani abun wanke kan kina iya karawa da shi, daga nan kuma sai ki samu man kitso ko man gashi ki shafama gashin duka.
Bayan nan ka karin abubuwan da ya kamata ki kiyaye idan kina son gashinki yarinka tsawo, sheki kumab da zama cikin lafiya batare da cututtuka suna yawan addabar shi ba.

Hanyoyin kulawa da Gashi

  1. Yawan wanke shi, kina iya hadawa da ganyen magarya ma
  2. Sharce shi akai akai
  3. Yin amfani da mai kamar su hulba, zaitun,da man albasa
  4. Yawan rufe shi don gudun kura tarika yawan shiga da sauransu.

Kammalawa

To kamar yadda kuka gani a sama matakan da muka ambata sune ake amfani da su wajen gyara gashi yayi kyau, sulbi da kuma kyalli, munyi post a baya na giki akan Abubuwan 12 da ke sa mace ta zama tauraruwar Girki kina iya duba shi, ku sance da www.Hausawasite.com.ng a koda yaushe mungode.