Skip to content
Home ┬╗ Labarai: Shugaba Buhari ya dawo gida bayan yaje sallah a garin daura

Labarai: Shugaba Buhari ya dawo gida bayan yaje sallah a garin daura

 

A wani rahoto da muka samu mun samu labarin cewa Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan shafe kwanaki a mahaifarsa Daura wadda take a garin katsina.

Tafiyar tasa ta kasance ne dalilin zuwa bikin sallah babba wadda aka gudanara a ranar talata inda yayi sallah a masallacin idi na garin daura da ke katsina.

Tafiyar tasa ta kasance Mai mahimmaci inda ya kaddamar abubuwa kamar haka.

Muhimman abubuwan da Shugaba Buhari ya kaddamar 

Kafin Shugaba Buhari ya isa a garin daura ya fara zuwa garin kano ne inda ya kaddamar da hanyar jirgin kasa wato layin dogo Wanda ya tashi daga kano zuwa kaduna.

Har ila yau Kuma bayan Zuwansa a garin daura ya hadu da gwamnan jahara katsina wato Aminu Bello Masari inda ya bashi Billion shidda Don habbaka kiwo a fadin jahara.

Bisa ga haka shugaban ya kaddamar da wajen kiwo na garin daura Wanda aka zagaya dashi inda a ke kiwon kaji, zomo dama sauransu.

Wanda wajen ya kasance na farko a fadin Nigeria inda zai taimaka wajen farfado da harkar kiwo a arewacin Nigeria dama kasar Nigeria bakidaya.