Skip to content
Home » Lalle: Amfanin lalle guda biyar (5) ga Mata

Lalle: Amfanin lalle guda biyar (5) ga Mata

Assalamu Alaikum jama’a idan akayi maganar lalle yawancin mata musamman matan hausawa sun san shi domin suna yin kunshi da shi, to wannan lalle yana da kyau ki kara rike shi da mutunci da daraja domin yana da matukar amfani ga kowace mace shin budurwa ce bazawara e koko yarinya ce.

Lalle

Duka yana da amfani a jikinsu, duba ga zuwa amfanin da yake ma mace na na’ima da sauransu ne yasa a wannan website ta Hausawa Site  muka ga ya dace muyi post akan shi kamar yadda a baya muniyi post kala kala na Girki kamar su Yadda ake Samosa , Farfesu , Cin-Cin , Tsire, da sauransu kina iya duba Fannin Girki .

Amfanin Lalle a Jikin ga mace

kamar yadda nayi matashiya a sama to ba tare da tsawaitawa ba zamu je ga Amfanin da yake da shi wanda gasu kamar haka.

Yana Tsotse Daudar Kai

Ko shakka babu lalle na daya daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajen wanke kai kuma yana taimakawa sosai wajen wankin.

Inda idan aka yi amfani da shi wajen wanke kai yana tsotse daudar kai ya kauda wani don-drops wata daudar da like da sauransu ya sashi yayi kyalli.

Yana sa Gshi Yayi Taushi

Kina son gashin kanki yayi taushi to lalle ya fado a nan domin daga ikin amfanin da yake idan aka wanke kai da shi shine yana sashi yayi tausi.

Wato zai rage ma gashin kaushi ya sashi yayi taushi da sulbi kwanin ban sha’awa ga mai kallo to kinga musamman yana da kyau amare su ringa amfani da shi da ma matana aure.

Lalle

Yana Maganin Sihiri

Lalle yana maganin sihirin da akayi ma mutum ko kuma kafaain a yi cikin ikon Allah inda yake karaya asiri lafiya lau

Yana Tsotse Cutar Kafa da Hannuwa

Daga cikin kuma muhimman amfaninsa a jikin mutum musamman mata da ke kunshi to yana tsotse cututtuka da dama da suke a kafar ko hannu na mutum, inda zaka fahimci haka shine zakaga ina aka gama kunshi ya dan tamuke fatar wajen.

Lalle na Taimakawa wajen Kwalliya

Kamar dai yadda aka sani musamman ga mata dolee sai da kwalliya duka ba budurwar ba, matar Auren ba kowace dole saida kwalliya to ana amfani da lalle kjamar yadda aka sani wajen kunshi kuma wanda yaawan yin kunshi ga mace yana banbace hannayenta da kafafuwanta dana maza saboda basu kunshi su.