Skip to content
Home » NECO Result: Yadda Ake duba Result na Jarabawar NECO

NECO Result: Yadda Ake duba Result na Jarabawar NECO

 

NECO
Jarabawar Neco kamar yadda aka sani sani tana daga cikin manyan jarabawar da daliban Nigeria suke rubutawa ta karshe a lokacin gama makarantar sakandire, a wannan post din zamu koya yadda zaka duba jarabawar ka da kanka koda wayarka ko ma computer dinka iya ka idan kana da printer kawai sai kayi printing.
Idan kuma ba kada printer sai ka ze wajen masu Sana’ar Printing da Photocopy su cire maka sakamakon ka wanda ka gano da kanka.

Matakan da zaka bi wajen duba Result dinka na jarabawar NECO

Ga matakai nan zan lissafa tare da bayani hadae da surorin yadda abun yake sai dai ya kamata kafin ka duba jarabarka ta Neco bayan ka tabbata ta fito to sai ka dauki Exam Card dinka sai kuma ka sayi Token dole sai da shi ake dubawa.
Karanta:

Mataki na Daya 1

Kunna wayarka ka ko computer dinka ka shiga browser kamar Opera ko Chrome domin shiga shafinsu na yanara gizo, zaka rubuta wannan address din ne a cikin browser gashi a kasa.
                                    Shafin Neco
Bayan ka ziyarci shafin zaka ga waje kamar yadda hoton sama ya nuna shashen da aka sa check Result  sai ka tafi wajen ka rubuta shekarar da kayi jarabawa

Shekara

Bayan ka zabi shekarar da kayi jarabawar sai ka tafi a mataki na biyu.

Mataki na Biyu 2

A mataki na biyu zaka sa yanayin jarabawar idan kai daga secondary kayi zaka zabi wajen ssce jun/july a fannin exam type.

Kalar Neco

Mataki na Ukku 3

Sai ka dauko token dinda ka saya sai ka rubuta a wajen wasu lambobi ne idan baka san inda zaka sayi token na necoi ba sai kayi mani magana a lambar waya 09037157675 ko ka turo mani email a fasahaltd@gmail.com sai in saida maka.
Neco Token

Mataki na Hudu 4

A wannan matakin sai ka duba registration number dinka ka rubuta ta a wajen itama daka rubuta sai ka tafi mataki na biyar.
Registration Number

Mataki na Biyar 5

Bayan ka gama rubuta registration number dinka kuma kka duba komai daidai ka sa sai ka danna inda aka rubuta Check Result  da ka danna zaka ga sakamakon jarabawar ka indai ya fito inshallahu.
                                    Duba Neco