Skip to content
Home » Yadda zaka sayi kaya daga China a kawo ma su har Gida

Yadda zaka sayi kaya daga China a kawo ma su har Gida

 

 

 

 

Yanxu duniya tacigaba musaamman zuwan internet yanzu da wayarka ma kana iya sayen kaya daga kasashe daban daban kuma a kawo maka gida duka wannan ba sabon a bu bane.

Akwai manyan wurare da yawa wanda ake sayen kaya a online kuma ba suna kawowa wadanda wanda suka fi fice sune na tan china, to a wannan post din inshallahu zan saka hanya yadda zaka gane abubuwan da kyau.

 

Bayani game da yadda abun yake

To a online dai akwai wurare da dama wanda ake sayen kaya amma a cikin wannan post din zamu doki fannin yan china a website din da ake kira Ali Express ka danna rubutun don shiga zaka ga ana saida kaya da yawa a ciki.

To Ali Express  dai katafaren kamfanin online ne dake kasar china suna saida ma shagunan dake china hajarsu a shafin dana bada link dinshi a sama, wato masu shaguna na kasar china zasuyi register dasu su ringa daura kayansu idan aka shiga aka saya suna da wani dan kamasho wanda masu shagunan suke basu.

To suna saida kayansu a fadin duniya gaba daya shiyasa yana da kyau in ka shiga zaka sayi abu ka natsu kaga mai shagon yana bada free shiping wato damar kawo ma kayan kyauta ba tare da an cajeka shiba in kuma ana biya duk lafiya lau sai ka biya duka gaba daya.

Yaushe Kaya Zasu Zo?

Kyanka ya danganta ga lokacin da suka samaka saboda ta jirgin ruwa ake kawo su zasu rubuta maka bayan ka  sayi abunda kake son ka saya a website din.
Amma mafi akasari daga sati ukku ne zuwa kamar wata hudu abun yayi tsawo sosai ma da sun iso post office wato gidan waya na garinku zasu kiraka kazo kaya sun iso ka amsa.
Shiyasa yana da kyau kasa number wayarka da address mai kyau don gudun afkuwar matsala duk da bata ika fariwa ba ma.

Ta wace hanya zan Biya kudi?

Zaka biya kudin abunda ka saya ta hanyar amfani da katin credit carad wato kamar irinsu Master Card ko Visa dasu ake amfani.
Shiyasa yana da kayau ka sa kudi a bankinka isassu yadda daka tashi  biya sai ka dauko katinka ka rubuta details na biyan ka biya zasu zare nan take.

Ya zan Fara Kuma a Ina zan sayi kayan?

A wannan fanni ina ba mai karatu shawara da idan zai iya ya fara saboda in kullun tsoro ya dame mu ba abunda zamu iya ga yar karamar haja kana iya dubawa ga link dinta

A nan inshallahu zan dan kara maka bayani tare da saka a hanya yadda zaka sayi kayan a cikin Ali Express din.

Mataki na Farko 1

Da farko dai ga link ga Shiga Ali Express  wajen sayayyar kaya zakaga kudin ko kuma farashin abun da zaka saya, a  kasa kuma zaka ga cikakken bayani game da abun wato description, kuma har ila yau zaka ga star yanayin yadda abun ya burge mutanen da suka taba sayen shi.

Wajen Sayen kayan

 

 

 

 

 

 

 

Sai ka Danna buy now domin kayi gaba.

Mataki na Biyu 2

A wannan mataki zakaga abunda ake cema Product Option wato zabi da aka baka na abun, a nan sai ka zabi kalar da kake sha’awa, yanayin girman shi, yanayin awon shi, kwara nawa kake so da sauran su duka a wannan fannin zaka same sa.
Launin Hajar

 

Mataki na Ukku 3

Da ka zo wajen da zaka yi da sign in da Email Address din ka in ka taba bude account da su, in kuma baka taba budewa ba kayi sayayya in kana da email address sai kayi register
Login

 

Karanta:

Mataki na Hudu 4

Daga nan a mataki na hudu za ya kaika inda ake nuna maka wasu matakai ukku da zaka bi wanda bayananka ne ake son samu.

 

Zaka kaga wajen ya kunshi Add Adress, comfirm da kuma Pay to a nan zaka cike addreshin ka, ka tabbatas da kuma a karshe biya.

Mataki na Biyar 5

Da ka gama mataki na sama zai tafi da kai a wajen Confirm a nan ne zaka tsaya ka natsu ka duba bayanan da ka bada dukansu daidai ne idan akwai kyara sai ka dawo baya ka gyara in babu kuma to shikenan sai ka danna Proceed.
 
Tabatar

 

 

Mataki na Shidda 6

A wannan mataki kuma daga shi kusan sai mataki na karshe, shi a nan zaka zabi hanyar biyan judinka ne in da katin bankin ka zaka biya shikenan sai ka zabi biya da kati.
Zabar hanyar biya

 

Mataki na Bakwai 7

A wannan mataki zaka danna add new wato ka sa katinka domin ko gaba ka tashi, a nan zaka sa sunan da ke jiki da wasu lambobi na gaba da kuma wasu lambobi na bayaka dai duba ka tabbatar ka cike abunda ake bukata a wajen.
Biyan kudi

 

Da ka gama sa komai lafiya lau zasu cire kudinsu daga banki su rubuta maka date din da kayan zasu zo zaka gani a karshen shafin sai ka jira post office na garinku ya danganta ga satuka ko watannin da kayan za suyi.

Kammalawa

A karshe dai sayayya online tana da matukar amfani kuma ana samun saukin kaya wani lokacin amma yana da kyau ka kula da wasu abubuwa musamman wajen cike address kasa inda kake kuma a wajen biya ka tabbatar kana da kudi a bankin ka isassu.