Skip to content
Home » YouTube: Bayani Game da YouTube da Yadda zaka Amfana da Shi

YouTube: Bayani Game da YouTube da Yadda zaka Amfana da Shi

 Youtube dai kamar yadda aka sani yana daya daga cikin shafuka na yanar gizo wanda a turance fanin Search Engines suke wato manema baya ga Google Search babu wani search wanda yazo na biyu kamar Youtube.

To sai dai kamar yadda ake gani abun takaici yawancin Yan uwa miusamman hausawa bamu amfani da shi inda ya dace kuma ana karuwa da shi sosai ni kaina kullun ina koyon abubuwa da yawa a youtube.

A dalilin haka ne a wannan post namu na wannan website mai address Hausawasite.com.ng muka ga ya kamata mu kawo maku irin rawar da yake tabukawa wajen habbaka kai wajen bincike da sauransu musamman ga dalibai kamar yadda a baya mun koya yadda ake download Videos na youtube a waya  kana iya duba shi da yadda ake download video na youtube a computer Duka kana iya duba su

YouTube

Minene YouTube?

YouTube manema ce (Search Engine) kamar Google wanda ake kallon bidiyoyi daban daban wanda wasu mutane suka kirkira, shima kamar Google duka abunda ka rubuta koda da hausa ne zaka samu amsa koma da wane yare ne indai babban yare ne.

karanta 

Yadda ake connecting Xender da Android a tura Files

Youtube an fara kirkirar shi ne a shekarar 2005, wasu ma’akatan kamfanin paypal suka fara kirkira shi a sillicon vally America sune chad Hurly, jewed karim da Steve Chen da suka kirkira shi ya fara suna sai Google ya sayi kamfani wannan shine takaitacen tarihin YouTube.

Yadda ake neman Video a YouTube

Akwai kala kalar video a youtube idan kana son shiga dole sai kana da data a cikin wayarka, daga nan sai ka shiga app din youtube kafara kallon video.
Amma idan a computer ne zaka shiga a cikin Browszer sai ka rubuta address din youtube  youtube.com
kamar yadda hoton kasa ya nuna.
YouTube
Da ka rubuta address din ka shiga zaka ga ya bude ya kawo ka wajen bidiyoyiyo a sama kuma zaka ga wajen da zaka nemi kalar bidiyon da kake so duka kana iya rubuta Hausa, Turanci koma Larabci da sauransu.
Youtube

Shawara ta akan yadda zaka koyi Abubuwa a Ciki

A saman inda ake rubta abunda ake nema idan misali kana son ka koyi yadda ake programming da turanci kana iya sa How to learn Programming for beginners ko kuma da hausa Yadda ake koyon Programming.

Idan kuma wasu manyan bayanai kake so kan misali wace software tafi wadda zakayi download a computer kana iya rubutawa da lamba a gaba misali 10 Best Graphic Softwares  da sauransu duka haka ake yi ga mai tambaya yayi a comment section yana a kasa zan amsa masa inshallahu.