Skip to content
Home ┬╗ MTN Data: Yadda Ake Samun 1.2GB akan naira Dari da Hamsin N150 a Tsarin mPulse na MTN

MTN Data: Yadda Ake Samun 1.2GB akan naira Dari da Hamsin N150 a Tsarin mPulse na MTN

 

Kamar yadda kowa dai ya sani MTN a cikin layuka sunfi tsarin data masu sauki kusan fiye da sauran abokan hamayyarsu Airtel, Glo da Etisalat musamman a Nigeria, idan ba’a manta ba a wannan Website ta WWW.HAUSAWASITE.COM.NG a baya munyi post akan yadda ake subscribtion na MTN 1GB akan N200. To a yau inshallahu zamu yi bayani akan wanda yafi sauki na 1GB akan N150 kacal.

Ya tsarin MTN 1.2GB A N150 yake?

Yadda wannan tsari yake shine yana a cikin jerin mutanen da suke a mPulse shi wani tsari ne wanda kamfanin ya bada dama ga yara musamman don habbaka iliminsu daga shekara 9 zuwa 15 inda yake sawaka masu data da sauran abubuwan da zasu taimaka masu a wajen karatu.
Karanta:

Ta ya zan samu Datar?

A karon farko tunda ba cikin tsarin kake ba zaka danna *344#  ka shiga zaya nuna ma allo kamar yadda hoton kasa ya nuna sai ka shiga na farko ka danna 1 kayi tura da sun sa maka congratulation ka koma tsarin shikenan sai kuma sayen data ya rage.

Shi kuma yadda zaka sayi data a wanna tsarin zaka danna *344# sai ka zabi lamba ta biyu 2, daka zaba zakaga tsarin data dinsu hadda wannan na N150 sai ka saya shikenan. Ga mai tambaya karin bayani da sauransu yana iya yi a fannin comment da ke kasa.