Idan mukayi magana akan data mai sauki ga dalibai ko kuma yan kasuwa ko ma ga duka gama gari kamar yadda muka san babban company na sadarwa MTN yana daya daga cikin masu bada data mai sauki rangwame da kuma rahusa daga cikin tsarin su wato plan dinsu akwai wanda ake cema Pulse ga wadanda basu sansi ba inshallahu a wannan post din zamuyi bayani dalla- dalla akan shi.
Table of Contents
ya tsarin MTN pulse yake?
Amsa mai sauki akan wannan tambayar ita ce yana daga cikin tsarukan Kamfanin MTN wanda suke bada damar kira a mtn zuwa mtn akan 11k/s kobo sha daya a duk sakon har zuwa mintin farko ga duk kiran da zakayi a gida Nigeria.
Bayan Haka kuma suna da tsarin data na Dare akan N25 sai kuma akwai na 1.5GB akan naira dari biyar a duk sati wadanna dama wasu sauran tsarukan sai ka shiga zaka gansu daya bayan daya
Ya zan shiga tsarin MTN pulse?
Yadda ake shiga wannan tsarin shine zaka bude wayarka ka danna wadannan lambobi *406*1# or *123*2*2#. ko kuma kana iya tura sako kasa 406 ka tura ma 131 shikenan. kana iya duba tsari mai sauki da muka koya a baya shima na mPulse wanda suke bada 1.2GB a kan naira N150
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin