Skip to content
Home » Maganin Fitsarin Kwance ga Manya da Yara

Maganin Fitsarin Kwance ga Manya da Yara

 

Fitsarin Kwance dai kamar yadda aka sanshi alada yara aka sani suna yinshi to amma a wani lokacin har ma manya suna yinshi kamar yadda a baya a cikin wannan website din mai albarka ta WWW.HAUSAWASITE.COM.NG muka kawo maku amfanin lalle da kuma yadda ake gyara gashi da shi.

To a yau inshallahu zamuyi magana ne akan masu lalurar ditsarin kwance da kuma matakan da zasu bi domin su magance shi cikin sauki.

Fitsarin Kwance

Mi ake Nufi da Fitsarin Kwance?

Fitsarin kwance dai shine farkawa bayan bacci musamman na dare a tarar  da fitsari wannan ya danganta ga manya ne ko kuma kananan yara.

Yadda Fitsarin Kwance yake aukuwa kafain mutum yayi shi, shine mafi yawanci lokacin da yake bacci zaya yi mafarkin ga ya nan an kai shi kewaye ko kuma ya je wani wuri yana yin fitsari to da mutum ya farka sai yaga kaya a jike.

Kamar yadda na ambata su yara kanana suna yin fitsarin kwance musamman daga shekara daya zuwa tasawarsu wanda wasun su ma idan aka sa suyi fitsari kafin kwanciya ma basu yi, amma ga yara bai cika zama illa ba.

Inda illar take ita ce ga babba wanda ya balaga namiji ne ko kuma mace ya kai ko kuma ta kai shekara sha takwas amma tana fitsari wasu ma manyan mutane ne to wannan matasala ce sai an nemi yadda za’a magance ta.

Yaya ake Maganin Fitsarin Kwance?

Ya kamata mai karatu ya san cewa nau’in fitsarin kwance kala biyu ne akwai wanda daga aljannu ne sai kuma akwai dayan kalar wanda shi kuma larura ce hakanan musamman ga manya masu fama da lalurar sugar ko kuma cututtuka masu kama da haka.

Kashi na Farko

To shi na farkon yadda za’a magance shi shine kafin mutum ya kwanta bacci ya tabbata ya karanta azkar wato addu’oi na bacci Wanda sune kamara haka: Zaka karanta suratul Falaq, Suratul Iklas da kuma suratul Nas sau ukku sai ka/ki tofa a hannu ka shafe jiki za’ayi hakan sau ukku.

Sai kuma a hada da sauran addu’oin bacci ayi kuma mutum ya rike azkar na safe da yamma yana yi to inshallahu cikin karamin lokaci za’a rabu da shi har abada.

Kashi na Biyu

Shi a wannan kashin wasu sanadiyyar ciwo ne abun ke samun su kamar masu ciwon sugar ko kuma wasu sanadiyyar rashin karfin mafitsarar ce ta rike fitsari idan ya taru to sai ta sake shi.
Yadda mutum zaya magance shi akwai hanya biyu mutum ya jaraba su yaga wane yayi masa na farko ya tabbatar kafin kwanciya yayi fitsari kuma ya ringa farkawa da daddare yayi fitsari.
Na Biyu kuma kuma ka samu abubuwan da suke gyara garkuwar jiki da kara ma jiki sinadarai kamar habbatussauda da zuma kana sha kafin kwantawa bacci da kuma shan tatacciyar zuma da safe kafin ka ci komai to inshallahu za’a samu saukin shi shima.