Skip to content
Home » Maganin Tari da Mura da sanyin Maza da Mata

Maganin Tari da Mura da sanyin Maza da Mata

 

Maganin Tari

Kamar yadda aka sani mura mafi yawanci tana da alaka da sanyi wadda duka da maza da mata suna yinta a lokacin canjin yanayi musamman na sanyi wani lokaci ma har zafi yana sa hakan, a yau a posu din mu inshallahu zamuyi magan akan yadda zaka magance mura a cikin dan karamin lokaci. domin ita wani lokacin sai ka ga ta dade mutum yana fama da ita taki tafiya.

Karanta: 

Maganin Fitsarin Kwance

Yadda ake Wanke Gashi da Lalle

Yadda ake maganin Tari

Da farko dai  zaka samu shayi mai zafi haka ka hada ya danganta koda ace lipton ne a cikinshi sai ka samu citta busassakamar kwara daya babba haka ka daddaka ta yadda zata fito sai ka zuba a cikin kofin shayin.

Bayan ka zuba a ciki sai ka ringa kurba ahanka kana sha yadda kana gasa makoshinka kana jin zafin cittar kayi haka sau biyu da safe da kuma kafin ka kwanta bacci lokacin dare inshallahu zakaga kana fidda majinar murar ta warke.
Idan kuma kana iya taunar citta ita kadai idan ka ga bayan dan lokaci tarin yana damunka sai ka saamu cittar ka ringa tauna ta har sai ka sotse ruwan ko kuma ka samu halawa ka hada su kana taunawa yadda taunawar zata yi maka sauki.