Skip to content
Home ┬╗ Tsarin Data mai sauki na MTN duk sati wadda ake bada Bonus

Tsarin Data mai sauki na MTN duk sati wadda ake bada Bonus

Kamfanin MTN ya kasance daya daga cikin manyan kamfanunnuka a Africa wanda suka yi ficce ta fuskar ayukan sadarwa ta zamani, a fannin Data ta waya musamman a Nigeria MTN ya zarce ma kowane layi saukin Data da kuma tsarin data da tsarin kira mai sauki.

Idan ba’a manta ba dai a baya munyi magana akan tsarin da ake sayen data 1.2GB akan naira N150,  da kuma Tsarin MTN pulse wadda suke saida data mai sauki.

A yau inshallahu zamu yi bayani akan farashin data ta MTN ta duk sati masu sauki wanda wasu daga cikinsu kamar ma bananza suka Bada su. Kuma duka suna hada su ne tare da Bonus domin kyautatama customominsu.

Tsarin Data ta MTN duk sati

Tsarukan datar gasu kamar haka tare da lambar da zaka danna domin ka saya kai tsaye a cikin wayar salular ka.

350MB + 350MB Bonus suna bada ta ne har tsawon sati akan Naira N300 idan kana so ka saya sai ka sako 102 zuwa 131.

1GB + 1GB Bonus ita ma suna bada ita har tsawon sati guda akan N500 idan za’a saya sai a tura sakon 142 zuwa 131.

6GB akan N1,500 itama ta sati sati ce idan za’a saya sai a tura sakon 143 zuwa 131.

2GB + 2GB Bonus akan N1,000 Itama datar sati ce idan zaka saye ta sai ka danna *131*105# daka danna zasu baka inshallahu

Shin Ina iya Yin komai da wannan Datar?

Tabbas inshallahu bayan ka  sayi datar zaka iya yin Browsing a yanar gizo kana kuma iya yin chatting facebook,  whattsapp, instagram, kuma kai harma kana iya kallon YouTube Videos da ita lafiya lau har tsawon sati guda musamman idan a wayarka akwai 4G to Inshallahu zaka ga saurin browsing saboda MTN sunyi Installing 4G.