Skip to content
Home » Sana’oin Gargajiya: Manyan Sanaoin Gargajiya na Kasar Hausa wanda Hausawa Ke yi

Sana’oin Gargajiya: Manyan Sanaoin Gargajiya na Kasar Hausa wanda Hausawa Ke yi

Sanaoin Gargajiya a kasar sun kasance wasu ababen dogaro da kai tun lokacin kaka da kakanni wanda suke ji don dogaro da kai.

A dalilin Sanaoin Gargajiya Hausawan zamanin da suka samu natsuwa wadata da kuma tattalin arzinkinsu tun kafin zuwan turawan yamma, wanda haka yasa koda turawa suka zo suka iske hausawa da aladunsu da kuma Sanaoinsu.

A yau a cikin wannan Website ta WWW.HAUSAWASITE.COM.NG zamu yi dubi zuwa ga ire-iren su, da kuma abubuwan da suka kunsa kamar yadda a baya mukayi sanao’oin hannu.

 

Ire- Iren Sanao’on Gargajiya na Hausawa

Sana’oin Gargajiya ga su kamar haka

  • Noma
  • Kiwo
  • Rini
  • Jima
  • Kira
  • Farauta

Karanta:  Sana’oin zamani da ake iya yi da waya 

Bayaninsu

Bayan mun ga Ire-iren su bari mu tafi zuwa bayaninsu daya bayan daya da kuma abubuwan da suka kunsa.

Noma

Sana'oin gargajiya

Noma na duke tsohon ciniki shine kirarin noma da Hausawa suke masa da dadewa.

A kasar hausa da babu wata babbar sana’a wadda zan ce maka kusan kowa yana yinta da ta wuce noma.

Inda mafi yawancin Kakanni suke amfani da noma domin cida iyalansu ta hanyar shuka abunda zasu ci.

Shi noma ya kasu ne zuwa gida biyu ga su kamar haka:

Noma Domin Cida Gida

Mafi yawancin noman da hausawa suke yi a kasar hausa da sukeyi musamman talakawan da wanda zasu cida gida ne kawai, wamda zaka ga mutum ya noma abunda zasu ci da iyalinsa kawai.

Misalin irin wannan shine wanda yake shuka hatsi irinsu masara, dawa, gero da ma sauransu wadanda ake sarrafawa zuwa abincin gargajiya.

Noma Domin Saidawa

Nau’i na biyu kuma shine wanda domin saidawa kadai ake yinsa wanda ba a iya ci kamar wadanda suke noma shukoki irin na auduga da kuma irinsu ridi da sauransu.

Kiwo

Ire-iren sanaoin gargajiya kamar kiwo

Kiwo na daga cikin sana’oi wanda suka shahara a wajen hausawa wanda suke yi tun kaka da kakanni.

Hausawa sun dade sun kiwata abubuwa na dabbobi daban daban kama tun daga mayan dabbobi zuwa kananan dabbobi.

Misalan wasu daga cikin dabbobin da hausawa suka dade sun kiwatawa sun hada da kaza, fannin raguna, shanu rakuma da ma sauransu.

Yawancin dalilin da yake sa ana kiwo shine domin a saida a samu kudi, wani lokacin kuma domin a yi aikin noma da su kamar su shanu wanda ake huda da su.

Rini

Sana’ar hannu ce wadda ake yi, yadda take shine ana canza ma kaya launi ko kuma kala ta hanyar rina su da sinarai.

Da dadewa hausawa sun dade suna rina kayansu wanda wadanda ke rini a hausa ana kiransu da marina.

Dalilin yinsa shine don a samu kudi da wanda rini har yanzu ana yinsa a yankunan hausawa daban daban a fadin duniya.

Jima

Tunda dadewa an dade duniya ana jima bama a kasar hausa kawai ba, inda ake saida abubuwan da ake hada sanadiyyar jima a kasuwa.

Jima tana nufin samun fata ta dabbobi a tsaftace ta yadda ta yadda za’a sarrafa ta zuwa abubuwan amfani.

Misalen abubuwan da ake hadawa daga jima sun hada da sulke, takalma, buzu da saurandsu.

Kira

Ko shakka babu kira na daya daga cikin sanaoin gargajiya na hausawa wanda suke yi tun zamanin kaka da kakanni.

Yadda ake kira shine za’a samu karfe a sa shi cikin wuta yayi ja yadda za’a sarrafa shi zuwa abubuwan amfani.

Wanda yake kira ana kiranshi da makeri shikuma wajen da ake kjirar ana kiranta da makera.

Misalan abubuwan da ake kerawa sun hada da abubuwan aikin gona akamar su lauje, hauya, gatari, mijagara da sauransu.

Akwai kuma abuwan yaki wanda suma a makera ake hada su kamar su Takobi, adda, makari mashi, kibiya da sauransu.

Farauta

Farauta na nufin kamo dabbobin daji ta hanyar halbo su ko kuma yi masu tarko yadda za’a kamasu.

Farauta ana yinta ne musamman don kamo nama daga daji domin a ci ko kuma a saiada a kasuwa ga wanda suka dauke ta a matsayin kasuwanci.

Wanda ya dauki farauta a matsayin kasuwanci ana kiranshi da mafarauci a kasar hausa.

Karanta:

Kasuwanci guda 10 wanda aka fi saurin samun kudi da su

Ire-Iren Sana’o’in Zamani 5 da ake yi da waya don samun kudi

Minene Bitcoin? 

Cryptocurrency da yadda ake samun kudi da shi

 

Kammalawa 

To a nan ne muka zo karshen wannan bayani akan sana’oin gargajiya wanda hausawa suke yi dpomin dogaro da kansu.

Wanda yake da tambaya ko kuma wani karin bayani yana iya yi a kasa wajen comment section.