Skip to content
Home » Sanao’in Hannu da ake saurin samun kudi da su

Sanao’in Hannu da ake saurin samun kudi da su

Har kullun sana’a tana da matukar amfani wajen taimakama mutum kuma akwai sana’oi hannu da ake samun kudi da su kala kala wanda wasu daga cikinsu nada saukin farawa watau da karamin jari ana iya fara su wasu kuma dole saida babban jari.

Kamar yadda ake cewa kar ka raina sana’a komin kankantarta da kadan ne ake tarawa su zama da yawa ba kuma wani mai kudi a duniya wanda ya tashi rana daya ya samu kudi ba tare da ya wahala ba.

Wace sana’a ya kamata in fara?

Wannan itace tambayar da dukkan wanda yake son fara wata sana’a yayi ma kansa, domin ita sana’a abu ce wadda zaka fara kuma kake gurin ka cigaba da yi har tsawon rayuwa idan domin dogaro da kai imma kai mai yaro ne, dalibi ne ko kuma magidanci.

To sai dai hanzari ba gudu ba ya kamat ka tambayi kanka wadannan abubuwan kafin ka fara wata sana’a ko kuma kasuwanci gasu kamr haka:-

  • Wace sana’a zan fara?
  • Shin ina da sha’awar fara wannan sana’ar?
  • Nawa zan tanada?
  • Ina zan koye ta?
  • Idan ni dalibi ne zan iya yinta ina karatu?
  • Ya zan inganta ta?
  • Shin suwaye zasu rinka saye?

Wadannan dama sauran wasu muhimman tambayoyi ya kamat wanda zai fara wani kasuwanci yai ma kansa kafin ya fara saboda da haka ne zai fahimci inda zai dosa a cikin harkatr.

Wasu daga cikin sana’oin da aka fi samu da su

Dinki

Sana’ar dinki ana samu da ita sosai saboda ita sutura dole ne kowa ya sa ta ka bukukuwa kuma ana yi kala kala, shiyasa zakaga teloli musamman a irin kasashe namu na Nigeria masu irin wadannan sana’oin suna samun kudi saboda kamar ga sallah aiki har ma yawa yake masu.

karanata: Sanaoin Mata wanda zasu iya yi a Gida domin su samu kudi

Kahinta

Sana’ar kafinta na daya daga cikin sanao’in da ake samun kudi da su musamman kafintocin da suke kera irinsu kujeru, gadaje lokoki da sauransu saboda yasnzu abu kadan idan za’a hada maka zakaji kudi ne da yawa’

Daga cikin kuma masu samun kudi sosai akwai wadanda suke da lwarewa a cikin sana’ar kuma suna da kayan aiki na sarrafa katakon zamani irinsi pla wood.

Karanta: 

Yadda Zaka samu kudi da abubuwan da ka iya da Computer su zama Sana’arka da inda zaka koye su

Cryptocurrency da yadda ake samun kudi da shi

Minene Bitcoin? Cryptocurencies da Abubuwan da ya kamata ka fahimta game da su

Yadda ake Samun kudi ta hanyar amfani da Internet a wayarka ko kuma a cikin computer din ka don bunkasar Kasuwanci

Sanaoin Mata wanda zasu iya yi a Gida domin su samu kudi