Skip to content
Home » Tarihin Dr Sani Umar Rijiyar Lemu da Da’awarsa

Tarihin Dr Sani Umar Rijiyar Lemu da Da’awarsa

Dr sani umar Rijiyar lemu
Idan ana maganar Duniyar Ilimi na Hadisai kai har ma da fannin Tafsiri a fadin africa ta yamma Dr Sani yana daya daga cikin manyan Maluman Sunnah wanda suka sadaukar da Rayuwarsu Gabadaya wajen yada sunnar Manzon Allah (S.A.W).
Har Kullun suna kokarin karantar da alumma game da yadda zasu daidaita alakarsu tsakaninsu da mahaliccinsu kai har ma yadda zasu kyara alaka tsakaninsu.
A dalilin Haka ne a wannan website mai Albarka yau muka zabi kawo maku tarihin babban Malami Wato Dr Sani Umar Rijiyar lemu wanda kowa yake yawan jin karatuttykan sa.

Tarihin

Tarihin Haihuwarsa da Kuma Kurciya

Cikakken Sunan Malam dai Shine Sani Umar Rijiyar Lemu an Haife shi ne a garin makkah a 1/7/1970  inda ya girma a Nigeria a garin Kano a wata unguwa da ake cema Yan Mata a cikin garin kano din, inda nan ne ya Himmantu sosai ta fuskar neman Ilimi  afarkon Rayuwarsa.

Karatunsa

Ya fara karatu ne a wata makarantar firamaren da ake kira da Khairul Bariyya Primary school wadda take a cikin garin kano a shekarar (1978 – 1983).

Daga nan kuma bayan kammala ta sai ya tafi zuwa secondary inda yayi (H.I.S) a wata sakandiren sahuci wadda take a garin kano a shekarar 1987 a nan ne yayi karamar sakndire.

Sai kuma ya wuce babbar sakandire a ta ilimi mai zurfi  a Gwale wato (Senior Islamic Studies) inda Cikin Ikon Allah ya samu gamawa da Distinction a cikin shekara ta 1980.

Tarihin makarantar dr sani umar rijiyar lemu

Karatun Jami’a

Malam ya samu digirinsa na farko da First Class a jami’ar da ke garin madina a saudiyya inda ya karanta B.A Hadith and Islamic Studies a shekarar 1994.

Ya kuma yi Masters na M.A Hadith and Islamic Studies inda nan ma ya fita da First Class a shekarar 2000.

Kuma daga bisani sai ya wuce zuwa Digiri na Ukku wato PHD inda ya kammala shi a shekarar 2005.da Distinction.

Tattanawar da akai da shi a BBC Hausa

Da’awarsa

Malam ya kasance daga Cikin manyan malamai da suka shahara a fadin africa dama duniya bakidaya inda a Nigeriya yana gabatar da karatuttukansa a masalatai kamar su masallacin kandahar, masallacin kwallaga dama sauransu