Skip to content
Home » Tsawon Gashi: Abubuwa guda 5 dake sa tsawon gashi

Tsawon Gashi: Abubuwa guda 5 dake sa tsawon gashi

Tsawon gashi ko shakka babu kowace mace tana son ta same shi, domin gashi mai tsawo yana sa kara ma mace kyau shin yarinya ce, Budurwa ce ko kuma matar aure.

A baya kamar yadda mukai magana akan yadda ake Yadda ake wanke gashi da lalle, to a yau zamu yi magana ne akan wasu mahimman abubuwan da ke sa tsawon gashi baya ga lalle.

Tsawon Gashi

Abubuwan da ke kara Tsawon Gashi

A binciken da masana sukayi sun gano cewa wadannan abubuwan na kara tsawon gashi kuma suna  da matukar amfani ga gashin ,mace har da ma lafiyar kai da jijiyoyin Ido..

Man Albasa

Man Albasa yana matukar amfani ga gashin mace kamar yadda masana suka fadi yana kara tsawo, laushi ke har ma yawan gashi yana karawa.

Ana son yawan shafa shi  da zaran kin wanke kanki.

Man Hulba

Hulba bama wai wajen karin gashi ba kawai tana da matukar amfani a jikin mace saboda tana daya daga cikin abun da take kara ma mace Ni’ima.

A fannin gashi kuma ko shakka babu ana son ariga yawan amfani da ita musamman bayan an sharce kai wajhen kitso.

Man Kadanya

Man Kadanya nada amafanin shi da yake yi a jikin mace mace saboda shi man kadanya yafi lafiyayyen man shafawa na Verselen da muke shafawa dadewa a jikin mutum.

Man kadanya na taimakawa wajen sa gashin mace yayi tsawo kuma yana kare shi daga saurin kamuwa da cututtuka da suke barazana a kai.

Karanta: Yadda Ganyen magarya Yake Gyaran jiki

Man Kadanya

Man Kadanya nada amafanin shi da yake yi a jikin mace mace saboda shi man kadanya yafi lafiyayyen man shafawa na Verselen da muke shafawa dadewa a jikin mutum.

Man kadanya na taimakawa wajen sa gashin mace yayi tsawo kuma yana kare shi daga saurin kamuwa da cututtuka da suke barazana a kai.

Man Kwakawa

Man kwakwa shi zaki ga yawan cin kamfanunukan da suke hada man gashi, Suna yawan hada na man gashi saboda matukar amfanin shi ga gashi..

Daga cikiin amfanin shin idan ana shafa shi a gashi sun hada da.

  • Maganin Amosanin kai
  • Yana kara sa sulbin gashi
  • A fuska yana maganin kuraje
  • Yana kara laushin gashi
  • Yana kara Bakin gashi

Man Zaitun

Shi dama man zaitun yana da matukar amfani, a fanin gashi ma kuma yana da rawar da yake takawa sosai.

Yawan shafa man zaitun a kai yana kara sa tsawon gashi da kuma kara inganta shi ta yadda zai kasance mai sulbi da kuma salki, kuma yana kara sa gwarin gashi.

Karanta :Yadda ake wanke gashi da lalle ga mata

                 Yadda Zaka Fara Kasuwancin Hada Man Gashi ko man kitso

                 Yadda ake wanke gashi da lalle ga mata

                  yadda ake hada ingantaccen shampo na gashi

Mai Wanda yake Taimakawa

Abubuwan da na ambata su a sama idan kinga suna maki wahalar samu to kofa a bude take kina iya tuntubarmu akwai wani mai wanda ya tattara su wanda na kitso ne.

Saboda kayan wani lokacin musamman a cikin wasu garuruwa suna dan wahalar samu to shiyasa saboda masu tuntubar mu muka ce bari mu hada shi wanda indai kina amfani da shi cikin ikon Allah zaki sha mamaki.

Ga hanyar da za’a tuntube mu a whattsapp ko kuma kira kamar haka zan ajee su a kasa.

Phone Number: +2349037157675

Email : fasahaltd@gmail.com

Kammalawa

Gashi shine yake kara fiddo mace kuma yana da matukar amfani a wajenta, musamman ga matan aure har ma ga wanda basu da auren.

Ga mai neman karin bayani tayi a comment section da ke a kasa.