Skip to content
Home » Abubuwan da ke taimakawa wajen zaman Hardar Qur’ani

Abubuwan da ke taimakawa wajen zaman Hardar Qur’ani

Hardar qurani kamaar yadda mukayi magana baya abu ne daya ke da falala a duniya da kuma ranar lahira wanda mahardata Qur’ani kamar yadda aka sani ko a duniya daban suke  indai wanda yayi wannan hardar domin neman yardar Allah ne yayi ta.

Abubuwan da ke taimakawa wajen Za,man Hardar Quran

Kamar yadda ,mukayi magana a baya akaan yadda ake hardace Qur’ani   a yau kuma inshallahu bayan an yi ta zamu kawo abubuwan da ke taimakawa hardar ta zanna da wanda za’a yi da kuma wadanda ya kamata mutum gujemawa.

Mi ke taimakama Hardar Qur’ani ta zanna?

A wurin na raba wadannan abubuwan zuwa gida biyu akwai wanda mutum ya kamata ya lazimta yana yi akwai kuma abubuwa marassa kyau da mutum ya kamata yayi iya kokari ya kaucemawa saboda hardar shi ta zanna.

Abubuwan da ya kamata mutum yayi

Addu’a

Adduar neman zaman karatun qurani wanda aka hardace

Na daga cikin abubuwan shine dai na farko mutum ya rike addu’a ya rinka rokon Allah ya taimaka mashi a wannana karatun Qur’ani da yake son ya hardace.

Ya kuma sa niyyar wannan karatun domin neman yardar Allah ne zai yi shi kuma ya rinka rokon Allah ya taimaka mashi akan wanna guri da ya saka a gaba.

Yawan karatu

Abu na biyu kuma shine ya kula kamar yadda na ambata a baya akan yawaita karanta qur’anin tare da samun abokai na gari wanda suke harda.

Samun abokan karatu na taimakawa kwarai da gaske wajen zaman harda saboda zai rinka samun hazaka ta hanayr ganin wancan yayi nima bari in dakge inyi a cigaba da gasa, daman haka ake so ayi gasa a wurin abun alkhairi ba abun banza ba.

Tuna Falalar karanta shi

Yawan tuna dumbin lada da mai karanta qurani yake samu a wajen Allah kamar yadda nassi ya tabbata duk idan mutum ya karanta aya daya yana da lada goma.

Yadda aabun yake duk harafin da mutum ya furta na wata ayar qurani indai domin Allah yayi zai samu lada goma, to ina ga mutum ya karanta sura ko kuma ya karanta izifi ko kuma fiye da haka a rana abun yana da falafala sosai don haka sai a dage a daura damara.

Abubuwan da ya kamata a guje mawa

Yawan sabo

Abubuwan da mai harda zai guje mawa

Wanda yake son hardar shi ta zanna to yana da kyau fa yayi kokari yaga ya gujema yawan aikata abubuwan sabo domin hakan na taimaka masa wajen zaman hardar tasa.

saboda shi sabo illa gareshi yana sa kasalar yin aikin lada, misali idan mutum ya aikata wani aikin laifi to zai hana shi yayi wani aikin lada wanda ya kamata yayi yaji abun yayi masa nauyi to kaga ya kamata ga ,mai son harda yayi kokari ya rage sabo ya ringa yawan tuba wajen Allah, Allah kuma ya gafarta mana baki daya, Ameen.

Rage yawan son more rayuwa

mai harda wanda yake son hardar qurani ta zanna mashi ya rinka kokari wajen nisantar abubuwan da zasu shagalar da shi akan hardar shi koda ba na sabo bane.

Duka abunda yaga bai kai mahimmancin ya tsaya yayi karatu ba to uya kauracemasa ya bar yinsa yaje wajen mai amfani yayi shi wanda shine karatun.

Kammalawa

Kamar yadda dai muka sha fada sai a dage wajen karanta littafin Allaah ta hanyar koyonshi saboda shimai koyo ma kusan lada biyu gareshi ta kokarin kakarewa da kuma ta karata qur’ani.

kaga abu ne mai mahimmaci ga rayuwar musulmi, a nan muka zi karshe wanda yake da wata tambaya ko kuma wani karin bayani yana iya yinsa a commen section wanda yake a kasa zan duba sai in gani mungode a cigaba da kasancewa da WWW.HAUSAWASITE.COM.NG  a koda yaushe.

Karanta:

Yadda ake bude YouTube Channel

Yadda ake Hardace Qurani

Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer