Skip to content
Home » Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta

Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta

Koyon Internet yana da matukar amfani kasan abubuwa da dama da suka shafi Internet wato yanar kizo domin cigaba ne wanda zamani ya zo da shi idan akayi amfani da shi yadda ya kamata yana taimakama sana’oi, kasuwanci ilimi da ma sauran sassan rayuwar dan dam daban daban.

A cikin wannan post din zamu yi magana akan yadda zaka iya internet ka samu saukin binciken abubuwa tare da yadda ita kanta fasahar take aiki a fadin duniya bayan kayi connect da internet din.

koyon internet

Ma’anar Internet(Yanar Gizo)

Internet wato yanar gizo na nufin jerin gwanin wasu computoci wanda suka hadu a fadin duniya ta yadda suke musayar bayanai a tsakaninsu.

Babu waanda a fadin duniya zai iya bugun gaba ya cema wai shi keda yanar gizo shi yake da komai ba haka abun yake ba ta kowa ce manyan computocin nike magana a sama inda na bada abuda take nufi wato servers kenan a turance.

Su wadannan servers din suna watsa bayanai na shafukan internet ne wato websites a duk fadin duniya yadda kowace computer zata iya samu kamar waya da sauransu kaga daga wata babbar computer wadda ta rike bayanai zuwa kanana to shine ake nufi da yanar gizo.

Rabauwar Shafukan Internet

Bayani akan rabuwar shafukan internet yanar gizo

Shafukan internet sun rabu da yawa amma ga wasu manyan fannoni guda ukku wanda na tantance domin saukin fahimta ga maia karatu.

Search Engine

Idan aka yi magana akan search Engine ana magana ne akan manema ta Internet wanda wasu na’uin shafuka ne na yanar gizo da zaka ziyarta domin neman bayanai akan wasu abubuwa.

Yadda ake neman bayanai a google

Misalansu sun hada da Google, YouTube, Bing da sauransu su dai kawai aikin da suke yi shine ka nemi wani bayani ko da turanci ko kuma da hausa akan wani abu ka samu suna bada amsa wasunsu a rubutu, bidiyo da kuma hotuna wasu kuma bidiyo zalla kamar yadda nabada misali da youtube a nan.

Amfani da irin wadannan search din yana da sauki saboda cigaban kimiyya a yanzu yakai kana iya rubuta masu da kusan kowane yare su baka amsoshi da dama.

Yadda zaka nemi abu a Search Engine kamr su Google.
  • Farko ka shiga cikin browser wadda kake da ita chrome ko opera amma chrome ta fi ita ce ta kamfanin
  • sai ka rubuta duk abunda kake nema da kowane yare zakaga shafin amsa.
  • Sai ka rsaya ka kula wane kake so Rubutu ko bidiyo sai ka zaba
  • Da ka shiga sai ka natsu kaga idan ka samu abunda kake nema in kuma baka samu ba sai ka fito ka kara nema.

Shafukan Rubuce- Rubuce

Sai kuma a fanni na biyu akwai wasu shafuka wanda sukuma zakaga rubuce rubuce zaka samu a cikinsu wadanda a turance ake cema su blogs.

Su shafuka ne wanda search engine wadanda mukayi bayaninsu a sama suke bada amsar abunda suka rubuta da sauran shafuka masu alaka da su kamar da kafafaen sada zunta,

Su kawai zaka samu rubutu ne akan wata kasida misali kamar yadda kake karantawa a yanzu to haka abun yake.

Kna iya duba post da kasa munyi bayani akan yadda ake bude wenbsite na blog tare da makan da ake bi dala- dala.

karanta : Yadda zaka bude karamar website na Blogger | Lesson 1

Kafafen sada Zumunta

yadda facebook yake da kuma yadda ake amfani da shi

Kafafen sada zumunta wani launi ne na shafukan internet wanda suke taka muhimmiyar rawa a rayuwar alumma wanda ake watsa hotuna bidiyoyi dama sauransu.

Kuma ana amfani da su wajen habbaka kasuwanci tallata kasuwanci dama sauransu saboda yawan mutanen da suke a ciki kuma da yanayin yadda ake saurin watsa bayanai da samun shi cikin hanya mai sauki batare da wani bata lokaci ba.

karanta:

Bayani game da tallar da facebook ke ma yan kasuwa da yadda zaka fara tallata hajarka

Kasuwanci: Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari

kammalawa

Kamar dai yadda nayi bayani ita internet kafa ce wadda take da amfani ga rayuwar alumma kuma ana karuwa da ita sosai musamman ga wadanda sukayi amfani da ita a hanyar da ya dace.

Kuma yanzu zani ya canza duk abunda kaga ya shigema to ka tafi internet ka nema kada ka ce dole saida turanci a’a koda yarenka na hausa lafiya lau daka tambayi google ko irinsu youtube inshallahu zaka samu amsar abunda kake nema a cikin sauki.

karanta :

Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

Abubuwan da ke taimakawa wajen zaman Hardar Qur’ani

Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su