Skip to content
Home » Maganin Ulcer da tayi Yawa(chronic) har abada

Maganin Ulcer da tayi Yawa(chronic) har abada

Maganin ulcer ga masu ita abun bukata ne sosai saboda illar da take haifar mu mutum idan tayi yawa a cikin jikinsa wanda zai kaga mutum har ma bai iya azumin ramadana wani lokacin.

A dalilin haka ne a cikin wannan shafin na Hausawasite.com.ng muka ga yakamata muyi bayani akan maganin ulcer yadda za’a rabu da ita har abada inshallah kamar yadda a baya mukayi magana akan maganin ulcer.

maganin ulcer

Matakan da zaka bi kafin fara shan maganin ulcer

Kafin in fara bayani akan magani bari.

Da farko dai idan ka san ulcer dinka tayi yawa chronic yadda tana wahalar dakai to ka kasance ka kiyaye sharuddan da likita yake hanaka kamar su.

  • Barin cin abinci da zafi sai ya huce
  • Brin cin abu mai yaji
  • Kauracewa abu mai tsami sosai
  • Rage yawan cin abu mai maiko

Wadannan abubuwan da muka lissafa dai a sama sunue ake son ka tabbatar ka yi iya kokari wajen kaurace masu.

Saboda idan ba haka ba zaka fara shan magani da  zaran ya fara yimaka aiki sai ka maida hannun agogo baya.

Yadda ake magance wadda tayi yawa

Yadda zaka magance ulce wadda ita kuma tayi yawa to abubuwan da ya kamata ka samu kamar haka:

  • Habbaatus saauda
  • Garin magarya

Yadda zaka hada kuma shine zaka samu yayan habbatus sauda masu kyau idan ma ka dan tauna su zakaji har yaji suke dan yi to ka samesu sai a samu turmi a daka su su daku.

Daga nan kuma sai ka samu garin magarya, bayn ka same shi sai ka sa a rika yi maka shayin habbatus sauda tare da garin magarya kana sha sai biyu safe da kuma marece inshallahu za’a samu waraka.

Kammalawa

Yana da kyau mai ulcer ya riqi ayaba yana yawan cinta bayan ya ci abinci dpmin hakan yana taimaka masa sosai wajen magance cutar.

kuma har kullun ga mai lalurar ulcer ya kula da abubuwan da muka ambata a baya wanda ko a asibiti yaje zasu gargade shi akansu. A nan muka kawo karshe mai karin bayani yana iya yinshi a comment section wanda yake a nan kasa.

karanta:

Maganin Ulcer: Yadda zaka magance gyanbon ciki ulcer Babba da karama

Maganin Tari da Mura da sanyin Maza da Mata

Maganin Fitsarin Kwance ga Manya da Yara

Amfanin Ganyen Kwanda da Cututtukan da yake Maganin su