Skip to content
Home » Samun kudi Cikaken Bayani Akanshi

Samun kudi Cikaken Bayani Akanshi

Samun kudi abu ne wanda ko shakkah babu ba wanda baya sonshi kuma kullun abun da mutane da ke fadin duniya sukeyi kenan akwai masu kudi akwai talakkawa suma dai kowa so yake ya samu kudi to yaya abun yake ne? nan take ake samun kudi ko ko akwai hanyar samu mai sauk?

Barka da kasancewa a tare da mu a wannan shafi na Hausawa SITE wanda kullun muke kokarin koyama jama’a yadda zasu samu sana’oi abubuwan wayewa na kimiyya da fasaha dama sauaransu, acikin wannan post din zamu yi magana akan shi kanshi neman kudi wato yadda ake samun su da yadda dabi’ar kudi take ga masu nema.

Yadda ake samun kudi cikin sauki nan take

Mi ake nufi da samun kudi?

Samun kudi yana nufin mutum ya samu dukiya ta yadda zaya gudanara da rayuwar sa a cikin walwala ba tare da wata takura ba ko kuma damuwa wadda zata kasance a tare da shi kuma ko a addinnin musuluncu ba haram bane mutum ya nemi kudi.

Hasali ma neman kudi ga wani akamar mai iyali dole ne ya wajaba a kansa ya nemo abunda zai cida yaransa domin hakki ne babba wanda Allah ya rataya masa a kansa ga yayansa da ya haifa.

To a addinance ba kowace hnaya kawai mutum yaga dama ba kawai ya bi ta hakanan wai ya ce zai samu kudi akwai wadda ta dace akwai kuma wadda bata dace ba duka ya danganta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Ya al’adar kudi take?

Ala’adar kudi shine ka zuba kudi kaga kudi bari in yima bayani yadda zaka gane bayanin sosai idan akace wannan abun na samun kudi ne to ko yaya ne dole yana da bukatar ka zuba jarinka ko yaya ne a cikinsa kai harma da lokacinka.

Kuma yawanci zaka ga idan mutum ya zabi zai yi wani kasuwanci ko kuma wata sana’a sai kaga ya fara tsoro ai wannan baya aiki malam sai ka zama namiji  a fannin neman kudi kanan zaka samu yadda kakeso in ba haka ba kuma ka fadi.

Dole ne ka dauki kaddara ka dauki asara ka fara wato ko kuma ince maka kayi kundunbala ka fara yawancin da ka fara zakaga kudi suna ta tafiya ba karakautawa to daman haka kudi suke daga nan ne zaka nemi yadda zaka rinka maida kudin da ka rasa da kuma ribar ka.

Yawancin kasuwanci ba da riba ake farawa ba ana farawa be da faduwa dakga baya ne ake samun riba sosai sanadiyyar hakuri da mutum ya sa wannan shi ake cema daukar riski dama bambancin masu kudi da mararsa kudi shine daukar riski kai kullun asara kake gani shikuma yayi kuru ya zuba ya fara sai Allah ya taimaka masa kuma.

Tunda kaji yadda ala’adar kudi take bari mu tafi akan abubuwan da zasu taimaka maka wanda yana da kyau ka sansu a wajen sana’arka ko kuma a fannin kasuwancin da kake game da kudi.

Daukar Lokaci

SAMUN KUDI BAYAN DAUKAR LOKACI

Tabbas neman kudi yana bukatar mutum ya dauki lokaci kafin ya same su ta hanyar sana’arsa ko kuma kasuwancinsa kamar yadda mai kudin africa Alh. Aliko Dangote yake cewa.

saida na dade ina tara dukiya kusan shekara 30 ina neman kudi amma yanzu matasa wasu so suke su tara dukiya nan take ba tare da shan wala ba.

Cewar Dangote

To ka gani abun yana da bukatar daukar lokaci mai tsawo wato naci da kuma maida hankali akan sana’a ko kuma kasuwanci da kuma rainon customomi yadda kullun za’a ringa dawowa wajen mutum saboda yadda yake da ingantattun abubuwa da kuma kyautata kayansa.

Yawancin wahalar da dan kasuwa ke shiga kuma yawancinsu suke sarewa a shekarun farko ne da fara wannan kasuwanci, mafi akasari kashi 90% na yan kasuwa idan suka wuce shekara ukku suna samun nasara sosai a kasuwancinsu musamman sana’aoin zamani.

karanta:

Yadda ake Samun kudi ta hanyar amfani da Internet a wayarka ko kuma a cikin computer din ka don bunkasar Kasuwanci

Yadda zaka kyara kasuwancinka da hanyar hotuna don jawo hankullan masu saye

Rainon Sana’a ko kasuwanci

Rainon sana'a

Kar yadda shufka take to shima kasuwanci haka yake yana bukatar aba shi abunda take so tare da kuma rainon shi tun yana jariri, karami har zuwa lokacinda ya girma ya zanna.

Zaka yi iya kokarinka duk da ace da karamin jari ka fara ka raine shi ko kuma idan da babbama ka fara to lafiya lau dai tarairaye shi yadda ya dace domin baka san inda zaka kai ba ta hanyar wannan kasuwancin.

Abubuwan da zaka kula dai da su sun hada da inganta abu , rike alkawari ga cwadanda suka kawo maka aiki, ihudda da mutane mai kyau yadda ya dace da sauransu suna taimakawa sosai domin cimma gurin neman kudin da kake.

karanta: Sana’ar Dinki da yadda zaka fara ta

Ingantanciyar Hanya

A nan hanya mai inganci ina nufin ka samu kasuwanci wanda na halal ne ba na banza ba ta hanyar cutar mutane da sauran makamtan abubuwa irin haka.

ka samu kasuwancin da hankalinka ya kwanta wanda doka ta yadda da shi ba wai wanda kawai da ka fara shi ba kwamnati ko kuma hukuma ta kama kayan sana’arka ta amshe a kaika gidan yari kaga wannan kasuwanci ne mai hadari.

To gaskiya hanya mai kyau tana daya daga cikin muhimman abubuwan dubawa a fannin kasuwanci saboda kusan shine ma za’a cema natsuwar kasuwa.

Karanta: yadda ake samun kudi online (Cikakken Bayani)

 Abubuwan da Suke dore Hanyar Samun kudi

Wadannan abubuwa wadanda zan lissafa su kamar haka suna taimakawa wajen yadda da kai dan kasuwa ga customers dinka ko kuma masu kawo maka aiki.

  • Gaskiya
  • Rikon Alkawari
  • Yin abun da gaske
  • Jure ma abubuwa na tsegumi
  • Neman gyara daga cusomoni da kuma gyarawar
  • Bincike akan sabbin abubuwan zamani na kasuwancin

Karanta :

Yadda zaka habaka kanka ta fuskar karatu da bincike a koda yaushe ta hanyar amfani a yanar gizo

Applications Biyar masu amfani na Kamfanin Google wanda suke da matukar amfani a rayuwar yau da kullun

Kammalawa

To kamar dai yadda bayani ya gabata akan bayani game da samun kudi to a nan abunda zan kara ba wani bane ba sosai samun kudi nada bulkatar juriya, hakuri, gaskiya da sauransu.

Kuma kamar yadda hausawa ke cewa babu maraya sai rago to kasuwanci na kwarazan mutane ne masu aiki tukuru, jarumai ba raggaye ba.

A nan zan tsaya idan kana da tambaya karin bayani ko kuma wani karin haske kayi shi a kasa wajen comment section.

Karanta:

 Yadda ake fara kasunacin hada man shafawa a samu kudi dashi sosai

Sana’ar Dinki da yadda zaka fara ta

Hanyoyi 5 da Ake Samun Kudi da su a YouTube

Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta